Zaben 2027: Tinubu Ya Kunyata Masoya, Ya Hana Fara Yi Masa Kamfen a Dukkan Jihohi

Zaben 2027: Tinubu Ya Kunyata Masoya, Ya Hana Fara Yi Masa Kamfen a Dukkan Jihohi

  • Fadar shugaban kasa ta nesanta kanta daga kamfen din zaben 2027 da aka fara a wasu jihohi, ta ce bai samu amincewa daga Bola Tinubu ko Kashim Shettima ba
  • An bayyana cewa fara tallan 'yan takara a yanzu ya saba da dokar zabe, kuma shugaban kasa bai amince da kaddamar da kamfen kafin lokaci ya yi ba
  • Gwamnatin Tarayya ta bukaci wadanda ke daukar nauyin kafa allunan hoton Tinubu da matarsa a jihohi da su dakatar da hakan nan take domin kiyaye doka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana rashin jin daɗinta game da fara kafa allunan siyasa kan zaben 2027 da ke bayyana hotunan Bola Ahmed Tinubu, matarsa da Kashim Shettima.

Fadar shugaban kasa ta yi magana ne bayan fara kafa hotunan Bola Tinubu da matarsa a wasu manyan tituna a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

Kamfen
Gwamnatin tarayya ta hana fara yi wa Tinubu kamfen. Hoto: Hassan Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi, 13 ga Afrilu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Fadar Shugaban Kasa, allunan kamfen da aka fara gani a birane kamar Abuja da Kano, na iya zama barazana ga tsarin dimokuradiyya da dokokin zabe na kasa.

Bola Tinubu ya bukaci a mutunta dokar kasa

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu da Shettima na godiya ga goyon bayan da jama'a ke nuna musu, amma ba su amince da kowanne irin kamfen da ya saba doka ba.

Fadar Shugaban Kasa ta ce dokar zabe a Najeriya ta haramta fara yakin neman zabe kafin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta fitar da jadawalin zabuka.

Punch ta rahoto cewa har yanzu shugaban kasa bai ba kowa izinin kaddamar da wani kamfen ko ya amince da amfani da kowanne irin kafar yada labarai domin hakan ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a

Tinubu ya bukaci a dakatar da kamfen 2027

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga dukkan mutane ko kungiyoyi da ke daukar nauyin kafa allunan su daina nan take, domin kauce wa sabawa doka da kawo cikas ga tsarin mulki.

Sanarwar ta jaddada cewa shugaban kasa da mataimakinsa na mai da hankali ne wajen aiwatar da ayyuka da manufofin raya kasa, ciki har da farfado da tattali, inganta rayuwa, da samar da tsaro.

INECC
Gwamnatin tarayya ta bukaci a jira INEC ta sanar da lokacin fara kamfen. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Yaushe za a fara kamfen din 2027?

Fadar Shugaban Kasa ta ce idan lokacin yakin neman zabe ya yi bisa tsarin da INEC za ta bayyana, shugaban kasa zai sanar da 'yan Najeriya matsayarsa game da zaben 2027.

A yanzu haka dai, gwamnatin Tarayya na nan a kan bakanta na ci gaba da hidima ga kasa tare da gujewa duk wani abu da ka iya sauya hankalin jama'a daga ci gaban da ake kokarin samarwa.

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ba 'yan Najeriya hakuri a kan kuskuren da ta yi.

Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ne ya yi magana a madadin Bola Tinubu bayan fitar da adadin wadanda aka ba mukamai.

Gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da adadin wadanda aka ba mukamai ne yayin da ake zargin an nuna wariya da wasu 'yankunan kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng