Abin Ɓoye Ya Fito Fili: Jerin Sunayen Yarbawa 140 da Tinubu Ya ba Manyan Muƙamai
- Zargin da ake yi cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana fifita yarbawa wajen naɗin mukamai a gwamnatinsa ya fito fili
- An bayyana sunayen yarbawa 140 tun daga kan mai girma shugaban kasa, waɗanda ke rike manyan muƙamai a gwamnati mai ci
- Sanata Muhammad Ali Ndume ne ya fara tattago wannan magana a wannan karon, inda ya ce naɗe-naɗen sun saɓawa doka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bayanai na kara fitowa kan zargin da ake wa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na fifita yarbawa wajen naɗin muƙamai.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Imran U. Wakili ya bayyana sunayen yarbawa 140 da ke riƙe manyan muƙamai a gwamnati mai ci.

Asali: Facebook
Imran ya wallafa jerin sunayen a shafinsa na manhajar X wanɗa aka fi sani da Twitter yau Asabar, 12 ga watan Afrilu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin gwamnatin Tinubu da fifita Yarbawa
Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa ne ya fara tado da zancen rashin adalci a naɗin muƙaman da Bola Tinubu ya yi tun da ya hau mulki.
Ndume ya yi ikirarin cewa yadda shugaban kasa ke naɗa muƙamai a gwamnatinsa ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Wannan batu dai ya tayar da kura, inda yan Arewa suka fara nuna damuwa kan lamarin, suna cewa su ne suka fi ba Bola Tinubu kuri'u a zaɓen 2023.
Fadar shugaban kasa ta yi amai ta lashe
Da farko fadar shugaban kasa ta wallafa jerin sunayen duka mutanen da aka naɗa daga Arewa da Kudu tare da musanta zargin fifita sani yanki a naɗe-naɗen gwamnati.
Daga bisani kuma fadar gwamnatin Najeriya ta goge sunayen tare da ba da hakuri saboda kuskuren da ta tafka a ciki, amma duk da haka ta ce zargin da ake yi ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
"Akwai damuwa," Sanata Ndume ya yi magana kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027
Amma takardun da matashin ya wallafa na ɗauke da da sunayen yarbawa 140 tun daga shugaban ƙasa, waɗanda ke rike da muƙamai a gwamnatin Tinubu.

Asali: Twitter
Sunayen yarbawa 140 a gwamnati mai ci
"Ga jerin sunayen Yarabawa 140 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada. Wannan ba korafi ba ne, hujja ce cewa abin ya faru don haka kada wani ya zo yana kokarin kare shi.
"Kuma babu wanda ya taba yin wani abu da ya kai wannan, yawan mukamai masu matukar muhimmanci da aka ba wa kabila daya, ba ma yanki gaba daya ba," in ji shi.
Za ku iya duba sunayen a nan.
Da gaske Tinubu ya kori shugaban INEC?
A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa Bola Tinubu ya tsige Farfesa Mahmud Yakubu daga shugabancin INEC.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Bwala ya bayyana cewa irin waɗannan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan yanar gizo ba su da tushe, kuma ƙarya ce tsagwaronta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng