Bayan Ganawarsu, an Tono Bidiyo da Ganduje ke Sukar Buhari kafin Zaben Tinubu

Bayan Ganawarsu, an Tono Bidiyo da Ganduje ke Sukar Buhari kafin Zaben Tinubu

  • An tono tsohon bidiyon Abdullahi Ganduje yana caccakar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan sauya kudi kafin zaben 2023
  • A cikin bidiyon, Ganduje na cewa Buhari yana son hana zabe ne, inda ya zarge shi da lalata jam’iyyar da ta tallafa masa wajen hawa mulki
  • Ganduje ya ce babu amfani a sauya takardun kudi a wancan lokaci, ya ce shirin na Buhari tamkar kokari ne na hana yin sahihin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - An sake dawo da wani tsohon faifan bidiyo da Abdullahi Ganduje ke sukar Muhammadu Buhari.

Shugaban APC yana sukar Buhari ne kafin zaben 2023 lokacin da yake kokarin sauya kudin takardun Naira a Najeriya.

Ganduje ya caccaki Buhari a wani tsohon faifan bidiyo
Tosohn bidiyon Ganduje yana sukar Buhari kafin zaben Tinubu. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Wani mai amfani da manhajar X, @IU_Wakilii shi ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa a yau Asabar 12 ga watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ziyarci Buhari a Kaduna

Matashin ya wallafa bidiyon ne yayin da Ganduje ya ziyarci gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna.

Tawagar jiga-jigan APC ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Ganduje, ta kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ziyarar ta zo ne bayan shugabannin jam’iyyun adawa na PDP da SDP sun ziyarci Muhammadu Buhari a garin Kaduna.

Ganduje ya gana da Buhari a Kaduna
An gano wani tsohon bidiyo da Ganduje ke sukar Buhari. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Bidiyon Ganduje na sukar Buhari daf da zaɓe

A cikin bidiyon, Ganduje na zargin Buhari cewa bai son a yi zabe ne shiyasa yake kokarin kawo matsala.

A cewarsa:

"Mutum ya yi takara ya yi takara bai ci ba, aka zo aka yi hadin guiwa ya yi nasara har ya yi shekara hudu ya sake cin zabe.
"Yanzu zai fita babu abin da ake yi illa jam'iyyar da ta zabe shi ya lalata ta, saboda da Allah yanzu mutum ya zama Habu na Habu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Atiku da El Rufa'i raddi mai zafi a gidan Buhari kan zaben 2027

Ganduje sun shiga kotu da Buhari

Ganduje ya kalubalanci matakin inda ya ce ba shi da wani amfani musamman a wancan lokaci inda ya tambayi dalilin son tabbatar da shi a daidai lokacin.

A cewar Ganduje:

"Menene amfanin wannan doka, meyasa ba za a yi ta bayan zaben ba, meyasa ba a yi ta shekara bakwai da rabi ba?
"Mu mun kai kara cewa ba mu yadda da wannan tsari ba saboda mun gane shiri ne na a hana zaɓe.
"A karar da muka shigar, babban kotu ta ce a dakata kuma a ci gaba da karɓar tsofaffin kudi har sai an gama wannan shari'a, abin ma ya wuce wai baka son wani ya ci zabe, a'a dimukradiyya ce ma baka so."

2027: APC a Kaduna sun marawa Tinubu baya

Kun ji labarin cewa masu ruwa da tsaki a APC a Kaduna sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku da El Rufa'i, Ganduje ya dura gidan Buhari da jiga jigan APC

Taron jiga-jigan APC a karamar hukumar Kachia ya mayar da hankali kan tsaro da ci gaba a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa SDP ba za ta iya kawo cikas ba ga APC mai mulkin jihar da kasa baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng