Sanata Ndume na Shirin Ficewa daga APC Ya Haɗe da El Rufai a SDP? Ya Yi Bayani da Bakinsa

Sanata Ndume na Shirin Ficewa daga APC Ya Haɗe da El Rufai a SDP? Ya Yi Bayani da Bakinsa

  • Sanata Ali Ndume mai wakiltar jihar Borno ta Kudu, ya ce ba shi da wani shiri na sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa SDP
  • Ndume ya ce gwamnatin APC ta gaza jawo waɗanda suka mata wahala a jiki, wanda hakan ya tilasta masu tunanin sauya sheƙa
  • Ya ce a baya ya ankarar da shugaban ƙasa illar watsar da waɗanda suka taimaka wajen kafa gwamnati, amma sai aka fara zaginsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Muhammed Ali Ndume ya bayyana cewa ba shi shirin sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa SDP.

Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Najeriya ya ce jiga-jigan APC da ke shirin sauya sheka an fusata su ne.

Sanata Ali Ndume.
Sanata Ndume ya ce ba zai bar APC ya koma SDP ba Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanatan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 11 ga watan Afrilun 2025 a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv.

Kara karanta wannan

Yadda darektan APC ya yi wani irin mutuwa a hannun ƴan bindiga a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya tattara ya bar APC, tare da komawa jam'iyyar SDP mai alamar doki.

Tun bayan sauya shekar El-Rufai, manyan jiga-jigai daga APC da sauran jam'iyyun siyasa a Najeriya suka mara masa baya, suka fara rungumar SDP.

Akwai raɗe-raɗin da ake cewa tsofaffin ministocin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na shirin haɗewa da El-Rufai a SDP.

Ali Ndume na shirin komawa SDP?

Da aka tambaye shi ko yana da shirin komawa SDP, Sanata Ali Ndume ya ba da amsa da "a'a."

Ya ce bai da wani shiri na sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP ko PDP, duk da ce-ce-ku-cen da ke kara yaduwa game da yuwuwar ƴan CPC na barin jam’iyyar.

Sai dai ya ce APC na da dalilan damuwa idan lamarin ƴan CPC da ake zargin su na shirin komawa SDP ya tabbata, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

"Ba za a yi biris da irin wannan barazana ba. Kowace kuri’a na da muhimmanci,” in ji shi.

Dalilan da ya sa ƴan siyasa ke barin APC

Ndume ya ce dalilin da ya sa wasu fitattun ‘yan siyasa ke shirin ficewa APC shi ne saboda ba a kula da bukatunsu ko saka su cikin tafiyar gwamnatin da suka taimaka aka kafa ba.

"Idan ba a biya wa mutane buƙatunsu ba, sai ka ga sun sauya sheka, musamman a Najeriya, za ka ga ƴan siyasa na tsalle-tsalle tsakanin jam'iyyu kuma ba su damu ba.

Ndume ya kara da cewa gazawar gwamnatin APC na jawo waɗanda suka taimaketa ta samu nasara, na daga cikin abubuwan da ke fusata ƴaƴan jam'iyyar.

"Shekaru biyu kenan da muka kafa gwamnati, amma mutane da dama na jin an watsar da su, ba sa samun damar ganin shugaban kasa.”
Tinubu da Ndume.
Sanata Ndume ya tuna lokacin da ya ankarar da Tinubu illar watsi da ƴan APC da suka taimake shi Hoto: @aonanuga1956/X
Asali: Facebook

Sanata Ndume ya ankarar da Tinubu

Ya kuma bayyana yadda aka maida martani mai zafi gare shi lokacin da ya yi kokarin sanar da shugaban kasa game da halin da ake ciki:

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari

“Maimaikon a saurari sakon, sai aka fara zagin mai sakon a jaridu. Wannan matsala ce babba, kuma tana da matukar hatsari,” in ji Ndume.

Ndume ya ja kunnen Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ndume ya gargaɗi Bola Ahmed Tinubu kan shirin jagororin adawa na haɗewa domin yaƙar APC a 2027.

Ndume ya ce wannan shirin haɗaka ba abin wasa ba ne, domin ba karamar barazana ba ce da tazarcen mai girma shugaban ƙasa.

Bugu da ƙari, sanatan ya ce ya kamata Tinubu ya damu idan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya tare da shi a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262