Atiku, El Rufai, Malami da Sauran Manyan Ƴan Adawa da Suka Ziyarci Buhari a Kaduna

Atiku, El Rufai, Malami da Sauran Manyan Ƴan Adawa da Suka Ziyarci Buhari a Kaduna

  • A ranar Juma’a, Atiku Abubakar na PDP ya jagoranci tawaga mai ƙarfi zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna
  • Duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai ba, amma Atiku ya bayyana ziyarar a matsayin gaisuwar Sallah bayan kammala Ramadana
  • Daga cikin waɗanda suka raka Atiku akwai fitattun mutane irinsu tsoffin ministoci, gwamnoni da manyan masu riƙe da muƙamai
  • Matashin dan siyasa daga Bauchi, Surajo Caps, ya shaidawa Legit Hausa cewa yanzu masu adawa da Atiku Abubakar za su fara hayya hayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin manyan shugabannin adawa a gidansa da ke jihar Kaduna, a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu.

Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya jagoranci waɗanda suka kai ziyarar.

Kara karanta wannan

Akwai wata a kasa: Kungiyar NCM ta gargadi 'yan Najeriya kan hadewar Atiku da El Rufai

Atiku ya magantu da ya ziyarci Buhari a Kaduna
Atiku da wasu jiga-jigan 'yan siyasa sun ziyarci Buhari a gidansa na Kaduna. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Don tabbatar da wannan ziyara, Atiku ya wallafa wani saƙo a shafinsa na X tare da wani bidiyo, a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Atiku ya ce da ya ziyarci Buhari

Bidiyon ya nuna lokacin da Muhammadu Buhari ya tarbi Atiku da tawagarsa cikin fara’a da barkwanci.

Fitattun ‘yan siyasa sun gaisa da tsohon shugaban ƙasar hannu da hannu, yayin da wasu suka durƙusa suna gaishe shi.

Atiku ya rubuta cewa:

“A matsayina na Waziri Adamawa, dole na kasance a Adamawa yayin bukukuwan Sallah. Na wakilci Lamidon Fombina (Adamawa) a wasu daga cikin bukukuwan Sallar.
"A yau, na samu damar kai gaisuwar Sallah bayan bukukuwan zuwa ga mai girma Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya daga 2015 zuwa 2023.
"Kamar yadda muka saba, ya sa ni dariya har hakarkari na suka fara ciwo saboda barkwancinsa masu sanya dariya.”

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsu, an tono bidiyo da Ganduje ke sukar Buhari kafin zaben Tinubu

'Yan siyasar da suka raka Atiku zuwa gidan Buhari

Daga cikin waɗanda suka raka Atiku akwai fitattun mutane irinsu tsoffin ministoci, gwamnoni da manyan jami’an gwamnati.

Kamar yadda aka gani a cikin bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta, waɗanda suka raka Atiku zuwa gidan Buhari sun haɗa da:

  1. Tsohon ministan sadarwa, Isa Pantami;
  2. Tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami;
  3. Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal;
  4. Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai;
  5. Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswan;
  6. Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow.

Mutane sun magantu kan ziyarar Atiku ga Buhari

Atiku ya ja tawagar 'yan adawa zuwa gidan Buhari na Kaduna
Atiku, El-Rufai da wasu jiga-jigan 'yan adawa sun ziyarci Buhari a gidansa na Kaduna. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin abubuwan da mutane ke cewa kan ziyarar su Atiku ga Buhari:

@Nedumcity_:

"Muna jiran ka shigo jam’iyyar mu ta LP."

@shuraim:

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Atiku da El Rufa'i raddi mai zafi a gidan Buhari kan zaben 2027

"Ina fatan wannan ganawa ta shafi yadda za a kawar da Tinubu a 2027."

@OliverNgodo:

"Mai girma, kai wani babban jigo ne a gare mu. Muna murna da gudunmawarka ga Najeriya. Saboda kai muna da kyakkyawan yakini, a kan komai. Muna ci gaba da addu’a domin ka zamo shugaban ƙasa a 2027. Komai zai daidaita."

@UmarFaruq1888:

"Wallahi, indai ka haɗa kai da wannan azzalumin, wallahi ba zan zaɓe ku ba."

@Emmanue68176622:

"Wannan ziyara za ta saka matsi da bugun zuciya a sansanin APC."

'Yanzu za su fara hayya hayya' - Surajo Caps

Wani matashin dan siyasa daga Bauchi, Surajo Caps, ya shaidawa Legit Hausa cewa yanzu masu adawa da Atiku Abubakar za su fara hayya hayya saboda sun ganshi tare da Buhari.

Surajo Caps ya ce:

"Duk da cewa wannan ziyarar girmamawa ce, da kuma yi wa tsohon shugaban kasar Barka da Sallah, amma ina nan da kai, sai 'yan adawa sun fara hayya hayya.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku da El Rufa'i, Ganduje ya dura gidan Buhari da jiga jigan APC

"Sanin kowa ne cewa, Atiku ya taka rawa a siyasar Buhari, kuma sun dade a tare, kawai dai suna da bambancin ra'ayi da jam'iyya.
"Don haka, wai don an ga mai girma Atiku a gidan Buhari, ba wani abin hayya hayya ba ne. Ko da ya ke, dole hankalinsu ya tashi, saboda sun ga tawagarsa ta jiga-jigan kasa."

Surajo Caps ya ce ganin Nasir El-Rufai, tsofaffin gwamnoni da ministoci, a tawagar, ya nuna cewa akwai gagarumin shirin da Atiku ke yi wa zaben 2027.

"Mu dai muna nan a kan bakanmu, ba gudu ba ja da baya, Atikun za mu yi, saboda mun san Allah ne ke ba da mulki, don haka zai dubi halin da muke ciki, ya ba mu Wazirin Adamawa."

Ga bidiyon ziyarar a ƙasa:

Ganduje, shugabannin APC sun je wajen Buhari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar jiga-jigan jam’iyyar APC zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

Ziyarar ta biyo bayan zuwan shugabannin jam’iyyun adawa PDP da SDP da suka hada da Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Kafin haka, Abdullahi Ganduje da wasu manyan jam’iyyar sun kai wa Gwamna Dikko Umaru Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.