2027: Jigon APC Ya Taso da Maganar Neman Ajiye Kashim Shettima, Ya Yi Gargadi
- Farfesa Haruna Yerima ya soki yunƙurin wasu 'yan Arewa da ke son a sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da wani a yankinsu
- Jigon jam'iyyar APC ya ce barazana ba ita ce hanyar da ta dace a siyasa ba, kuma hakan zai iya dagula tsarin rabon mulki da aka gina tun 1999
- Yerima ya tunatar da rawar da 'yan Arewa ta Tsakiya suka taka a tarihi, yana mai cewa ba su fuskanci wariya a shekaru 65 ba da aka yi a Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan majalisa, Farfesa Haruna Yerima, ya yi kaca-kaca da wata ƙungiyar Arewa ta Tsakiya da ke neman a maye gurbin Kashim Shettima.
Kungiyar ta bukaci a maye gurbin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ɗan yankinsu a 2027.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Yerima ya ce yunƙurin ba daidai ba ne, yana mai cewa hakan yana da haɗari ga tsarin siyasa da aka dade ana ginawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fitar da wannan sanarwa ne a Abuja ranar Alhamis, yana mai jan kunnen masu neman sauya Shettima da su dena yin barazana ga Shugaba Bola Tinubu.
Yerima: Bai kamata a sauke Kashim Shettima ba
Farfesa Yerima ya ce tun daga 1999 tsarin mulki tsakanin Kudu da Arewa yana tafiya lafiya, inda shugabanni ke aiki da mataimaka na tsawon shekaru ba tare da sauyawa ba.
Trust Radio ya rahoto Yerima ya ce:
“Obasanjo ya yi aiki da Atiku shekaru 8, Jonathan da Namadi Sambo shekaru 6, Buhari da Osinbajo shekaru 8. Me ya sa yanzu za a nemi a sauya Shettima?”
Yerima ya ce Tinubu ya zaɓi Shettima ne bisa la’akari da ƙwarewarsa da fahimtar juna tsakaninsu, kuma yana gudanar da aiki cikin ƙwarewa da biyayya.
Binciken Legit Hausa ya nuna Jonathan da Namadi sun yi aiki ne na tsawon shekaru biyar daga 2010 zuwa 2015 da APC ta karbi mulki.
Maganar yin barazana ga Bola Tinubu
Farfesa Yerima ya ce barazanar da kungiyar Arewa ta Tsakiya ke yi wa Tinubu ta cewa za su janye goyon bayansu idan bai zaɓi ɗan yankinsu a matsayin mataimaki ba, ba siyasa ba ce.
Ya ce:
“Zaɓen mataimaki zabi ne na shugaban ƙasa. A tilasta masa wanda bai yarda da shi ba, ba zai haifar da da mai ido ba.”
Yerima ya ce ba a ware Arewa ta Tsakiya ba
A karshe, Farfesa Yerima ya karyata zargin cewa Arewa ta Tsakiya na fuskantar wariya na shekaru 65.
Ya bayyana cewa manyan shugabannin soja biyu – Janar Yakubu Gowon daga Filato da Janar Ibrahim Babangida daga Neja – duk daga yankin suke.
Ya ce:
“Gowon ya mulki Najeriya shekaru 9, Babangida kuma shekaru 8. To wace irin wariya ce za a ce sun fuskanta?”

Asali: Twitter
Yankin Shettima sun ce an ware su a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan majalisu da suka fito daga yankin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima sun ce a ware su a shirin noman Tinubu.
Shugaban 'yan majalisun yankin, Sanata Muhammad Danjuma Goje ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da suka yi a Abuja.
Sanata Danjuma Goje ya ce an shirya wani shirin noma na musamman amma ba a dauki ko jiha daya daga jihohin Arewa maso Gabas ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng