"Ni ma Zan Lallaba," Ndume Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Manyan Ƴan Siyasa ke zuwa Wurin Buhari

"Ni ma Zan Lallaba," Ndume Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Manyan Ƴan Siyasa ke zuwa Wurin Buhari

  • Sanata Ali Ndume ya ce ƴan Najeriya na kai wa Muhammadu Buhari ziyara ne saboda yana ɗaya daga cikin tsofaffin shugaban ƙasa
  • Ndume ya bayyana cewa shi kansa yana da niyyar zuwa gidan Buhari, yana mai cewa hakan ba sabon abu ba ne a Najeriya
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da wasu tsofaffin gwamnoni sun ziyarci Buhari a gidansa da ke Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammed Ali Ndume ya bayyana cewa shi kansa ya na shirin kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara.

Ndume ya ce ziyarorin da mutane kai wa Buhari ba abin mamaki ba ne domin ya zama uban ƙasa kuma mutum ne da yake da ƙima musamman a Arewacin Najeriya.

Buhari da Ndume.
Sanata Ndume ya ce zai kai wa Buhari ziyara Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanatan ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya aka yi da shi a gidan talabijin na Channels tv cikin shirin siyasa a yau ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya ja tawaga zuwa wurin Buhari

Kalamansa na zuwa ne a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ka wa Buhari har gida jiya Juma'a.

Atiku ya jagoranci tawaga mai karfi ta ƴan adawa da ta kunshi tsofaffin gwamnoni irinsu Malam Nasir El-Rufai da Aminu Tambuwal zuwa wurin Buhari.

Da aka tambaye shi kan wannan ziyara, Sanata Ali Ndume ya ce a zahirin gaskiya shi kansa zai ziyarci Muhammadu Buhari nan ba da jimawa.

Ne yasa ake zuwa wurin Buhari a Kaduna?

"Maganar gaskiya ni ma zan je, bari ka ji, ko kuna so ko baku so, Buhari na ɗaya daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasa kuma wannan ziyarorin da ake kai masa ba sabon abu ba ne."
"Idan za ku iya tunawa bayan ya mika mulki ga Bola Tinubu, ya koma Daura da zama. Mutanen mu haka suke, idan ka duba Obasanjo na yawan karɓar baƙi, haka ma Babangida.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Atiku da El Rufa'i raddi mai zafi a gidan Buhari kan zaben 2027

"Mutum ɗaya da za ka ga ba a yawan kai masa ziyara shi ne Jonathan, amma duk sauran tsofaffin shugabannin ƙasa za ka ga ƴan Najeriya suna kai masu wannan ziyara ta ban girma.

- Sanata Ali Ndume.

Ali Ndume.
Ali Ndume ya ce har yanzu Buhari na da ƙim a wurin ƴan Najeriya Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Twitter

Sanata Ndume na shirin ziyartar Buhari

A cewar Ali Ndume, tururuwar da mutane ke yi zuwa wurin Buhari ba abin mamki ba ne kuma shi kansa yana shirin zuwa saboda yanzu ya baro Daura ya dawo Kaduna.

Da aka tambaye shin kan dalilin da zai sa ya kai wa Buhari ziyara, Ndume ya ce:

"Ziyara ce ta kai da kai, alaƙa ta da Buhari ta wuce siyasa, duk da ba mu da dangantaka ta jini amma ina kyakyyawar alaƙa da shi, haka ma Bola Tinubu, mun jima tare," in ji shi.

Buhari zai sake goyon bayan Tinubu?

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ndume ya ce akwai damuwa idan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

'Matsalar da za ka fuskanta idan Buhari bai tare da kai': An tsoratar da Tinubu

Ndume ya ce ya kamata shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga damuwa idan Muhammadu Buhari bai goyi bayansa ba.

Sanatan Borno ta Kudu ya jaddada cewa har hanzu Buhari na da ƙima da daraja musamnan a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262