‘Matsalar da Za Ka Fuskanta idan Buhari bai Tare da Kai’: An Tsoratar da Tinubu

‘Matsalar da Za Ka Fuskanta idan Buhari bai Tare da Kai’: An Tsoratar da Tinubu

  • Sanata Ali Ndume ya ce Tinubu ya kamata ya shiga damuwa idan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai goyi bayansa ba
  • Ndume ya bayyana cewa duk da Buhari na da kuri’a daya ce kacal, yana da farin jini sosai a Arewacin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan ‘yan siyasa na CPC na shirin ficewa daga jam’iyyar APC
  • Buhari ya jaddada cewa zai ci gaba da kasancewa cikin APC duk da ficewar El-Rufai da wasu daga cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume ya yi magana kan tasirin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan zaben 2027.

Ndume ya ce ya kamata shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga damuwa idan Muhammadu Buhari bai goyi bayansa ba.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Ndume ya gargadi Tinubu kan tasirin Buhari
Ndume ya shawarci Tinubu ka da ya yi wasa da tasirin Buhari. Asiwaju Bola Tinubu, Mohammed Ali Ndume, Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Ndume ya ce ko da yake Buhari kuri’a daya yake da shi, amma yana da farin jini matuka a Arewacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku, El-Rufai sun ziyarci Buhari a Kaduna

Wannan na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jagoranci manyan ‘yan adawa zuwa gidan Buhari a Kaduna.

Tsohon dan shugaban kasar ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke jihar Kaduna.

Atiku ya jagoranci manyan mutane ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal zuwa gidan Buhari.

Daga cikinsu kuma akwai Sheikh Isa Ali Pantami da Abubakar Malami wadanda su ma suka kai ziyarar Sallah ga tsohon shugaban.

Ndume ya fadi matsalar da Tinubu ka iya fuskanta game da Buhari
Sanata Ali Ndume ya gargadi Tinubu kan tasirin Buhari a Arewa. Hoto: Bayo Onanuga, Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Ndume ya fadi tasirin Buhari a Arewa

Sanata Ndume ya bayyana cewa shi ma yana shirin kai wa Buhari ziyarar girmamawa domin nuna kima da darajarsa.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

Ndume ya ce:

"Biyo bayan shekaru takwas da Buhari ya yi a mulki, farin jininsa ya ragu amma har yanzu ba za ka raina shi ba.
"Bin Buhari a Arewacin Najeriya kamar wani addini ne, saboda haka Tinubu ya kamata ya damu.
"Idan Buhari zai zo nan yanzu, za ka ga mutane na kokarin ganin sa, ciki har da masu sayar da kayan lambu.
"Tinubu ya kamata ya damu idan Buhari bai goyi bayansa ba, domin kowacce kuri’a na da mahimmanci."

Ndume ya gargadi Tinubu kan wasa da kuri'arsa

Ndume ya ce abin damuwa ne ace Buhari bai goyon bayan Tinubu saboda zai iya jawo amsa matsala, cewar TheCable.

A cewarsa:

"Ni ma Tinubu ya kamata ya damu da matsayin da nake da shi, domin ina da kuri’a daya kamar Buhari."

Kaduna: Jiga-jigan APC sun marawa Tinubu baya

Kun ji cewa masu ruwa da tsaki a APC da ke Kaduna sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari

Jiga-jigan a karamar hukumar Kachia suka ce sun mayar da hankali kan tsaro da ci gaba a yankin karamar hukumar da ke jihar.

Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa SDP ba za ta iya kawo cikas ba ga jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng