El Rufai Ya Yi Magana, Ya Faɗi Dalilin Zuwan Atiku da Manyan Jiga Jigai Wurin Buhari

El Rufai Ya Yi Magana, Ya Faɗi Dalilin Zuwan Atiku da Manyan Jiga Jigai Wurin Buhari

  • Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya ja tawaga zuwa wurin Muhammadu Buhari ne domin yi masa barka da sallah
  • Tsohon gwamnan ya bukaci ƴan hamayya su kwantar da hankula, ka da su hana kansu barci domin ziyarar ba ta da alaƙa da siyasa ko batun zaɓe
  • A ɗazu ne Atiku, Tambuwal da manyan 'yan adawa suka ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna kuma jigo a jam'iyyar SDP, Malam Nasir El-Rufai, ya yi ƙarin haske kan ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

El-Rufai ya shawarci abokan hamayya da kar su damu da ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu tsofaffin gwamnoni suka kai wa Buhari a gidansa da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Akwai wata a kasa: Kungiyar NCM ta gargadi 'yan Najeriya kan hadewar Atiku da El Rufai

Atiku da Buhari.
El Rufai ya yi magana kan ziyarar da Atiku da tsofaffin gwamnoni suka kai wa Buhari Hoto: @BuhariSallau
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya yi wannan bayani ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook jim kaɗan bayan ziyarar a yau Juma'a, 11 ga watan Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Nasir ya bukaci ƴan adawa da kar su hana kansu barci saboda wannan ziyarar domin ba ta da alaƙa da siyasa.

Me ya kai Atiku, El-Rufai wurin Buhari?

Ya ce wannan ziyara da suka kai wa Muhammadu Buhari bayan ƙaramar Sallah ba ta da alaka da siyasa ko batun zaben 2027, illa alakar ‘yan’uwantaka da hadin kai.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana mutanen da tawagar da ƙunsa da suka haɗa da, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsofaffin gwamnoni.

Tsofaffin gwamnonin sun haɗa da Aminu Tambuwal (Sokoto), Achike Udenwa (Imo), Gabriel Suswam (Benue), Nasir El-Rufai (Kaduna da sauransu.

Da yake bayyana dalilin wannan ziyara, El-Rufai ya ce sun je wurin Buhari ne domin yi masa barka da sallah, idan suka yi sallar Juma'a tare a Kaduna.

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsu, an tono bidiyo da Ganduje ke sukar Buhari kafin zaben Tinubu

Atiku da Buhari.
Atiku, El-Rufai da wasu tsofaffin gwamnoni sun ziyarci Buhari Hoto: @BuhariSallau
Asali: Twitter

El-Rufai ya tsokani abokan hamayya

"Mun je Kaduna domin gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Mun halarci sallar Juma’a a masallacin Yahaya Road sannan muka ci abincin rana tare a gidan Buhari.
"A hakikanin gaskiya, ba sai abokan hamayyarmu sun damu ko su hana kansu barci ba, ba batun siyasa ba ne, zumunci ne da ƴan uwantaka.
"Tun da ana ganin mu ‘yan siyasa ne marasa tasiri, ba wani abin damuwa ba ne, mun yi sallah da cin abinci tare da jagoranmu.”

- Malam Nasir El-Rufai.

Wani ɗan APC a Kaduna, Ibrahim Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan ziyara tana da alaƙa da siyasa ko da kuwa sun musanta haka.

A cewarsa, yana tunanin hakan na ɗaya daga cikin dabarun El-Rufai na koƙarin kwace mulkin Kaduna daga hannun Malam Uba Sani.

"Gaskiya ni dai ban yarda babu siyasa a wannan ziyara ba, ka duba tawagar ka gani, dole akwai wata a ƙasa, lokaci zai fayyace komai," in ji shi.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

Haɗakar su Atiku ba za ta yi tasiri ba

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan Majalisa a jihar Legas ya ce duk wata haɗaka da ƴan adawa za su yi, ba za su iya kayar da Bola Tinubu ba.

Olusola Sokunle ya ce matukar shugaban kasa, Bola Tinubu ga nemi tazarce, haɗakar Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ƴan adawa ba za ta taɓuka komai ba.

Tsohon ɗan Majalisar ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa kokarinsa na gyara kasar, yana mai cewa 'yan Najeriya suna ganin kokarin da ya ke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng