"Zan ba Gwamna Mamaki," Sanata Nwoko Ya Yi Ƙarin Haske kan Jihar da Ake Shirin Kirkirowa
- Sanata Ned Nwoko ya sha alwashin cewa zai ba Gwamna Sheriff Oborevwori mamaki kan batun kirkiro jihar Anioma
- Ɗan majalisar datawan mai wakiltar Delta ta Arewa ya ce gwamna da muƙarrabansa ba su goyon bayan kudirinsa
- Nwoko ya bayyana cewa sai da ya gana da shugaban kasa da manyan APC kan jihar da yake so a kirkiro kafin ya sauya sheƙa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta - Sanata mai wakiltar yankin Delta ta Arewa, Hon. Ned Nwoko, ya bayyana cewa zai ba Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, mamaki dangane da batun ƙirƙiro sabuwar jihar Anioma.
Ned Nwoko ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Ogwashi-Uku da ke karamar hukumar Oshimili ta Arewa.

Asali: UGC
Leadership ta ce sanatan ya halarci taron da kungiyar mata ƴan APC tare da hadin gwiwar Rita Daniels Single Parenthood, Girl Child Initiative, da Regina Daniel’s Charity and Dev Foundation suka shirya.

Kara karanta wannan
"Na yi wa Allah alƙawari," Gwamna Alia ya yi magana da aka fara raɗe raɗin zai bar APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Delta bai goyon bayan Ned Nwoko
Ya bayyana cewa Gwamna Oborevwori ya shaida masa cewa ba zai mara masa baya game da kudirin ƙirƙirar Jihar Anioma ba.
Sanata Nwoko ya yi zargin cewa hadiman gwamnan gaba ɗaya ba su goyon bayan wannan yunkuri saboda son rai da tsoron rasa kujerunsu.
A kalamansa, ya ce:
“Yanzu an kai matakin sauraren ra’ayoyin jama’a bayan an karanta kudurin a karo na biyu. Bayan haka za a dawo da shi majalisar dattawa don karatu na uku sannan ya je hannun Shugaban ƙasa don amincewa.
Sanatocin Delta ba su san fa'idar kirkiro jihar ba
Nwoko ya kara da cewa tun daga Sanata Osakwe, zuwa Nwaoboshi da Okowa, babu wanda ya yi kokarin ganin an samar da sabuwar jiha saboda tsoron raba Delta da rashin fahimtar fa'idodin hakan.
“Fa’idojin ƙirƙirar sabuwar jiha sun hada da samun gwamna biyu, mataimaka biyu, karin ‘yan majalisa da ci gaba daban-daban. APC ce kadai jam’iyyar da za ta iya tabbatar da wannan buri,” in ji shi.
Shugaba Tinubu ya amince da ƙirƙiro Anioma?
Game da dalilin sauya shekarsa daga PDP zuwa APC, Sanata Nwoko ya ce ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 1 ga Janairu, 2025.
A cewarsa, bayan haka ya gana da Shugaban Majalisa da sauran manyan ‘yan APC da suka shawarce shi cewa idan yana son a rungumi batun jihar Anioma da gaske dole ne ya shiga jam’iyyar.

Asali: Facebook
“Na yanke shawarar shiga APC domin batun ƙirƙirar Jihar Anioma ya zama haƙƙinsu. Dukkan ‘yan APC a kwamitin sun nuna goyon bayansu,” in ji Nwoko.
Sanatan ya yi ikirarin cewa Gwamna Oborevwori ma yana son shiga APC, yana mai kira ga al’ummar Delta su riga kowa shiga jam’iyyar domin samun madafun iko a zabukan gaba.
Babban jigo a Delta ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan majalisar wakilai a jihar Delta, Hon. Nicholas Ossai, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Babban jigon siyasa a jihar Delta ya bayyana cewa ya zaɓi haɗewa da APC ne domin marawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu baya.
Tsohon dan majalisar ya ce manufofin Tinubu suna da muhimmanci wajen bunkasa kasa, idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ya samu a Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng