Buba Galadima: 'Dalilin da Ya Sa Buhari bai So Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa ba'
- Jagora a NNPP, Buba Galadima ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya haddasa ficewarsa daga cikin jam'iyyar APC
- Ya ce tun da farko, shugaba Buhari ya yi ƙoƙarin a cire shi daga cikin kwamitin amintattu na jam’iyya, amma Bola Tinubu ya ƙi amincewa da hakan
- Injiniya Buba Galadima ya ƙara da cewa ba zai sake komawa APC ba, duk da cewa yana da kyakkyawar alaka da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jagoran a NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam’iyyar APC ba, duk da kasancewar yana da kyakkyawar alaka da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ya kara da bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya samu nasara a zaben 2023 ba.

Kara karanta wannan
"Ya ɗauka ni ne," Abin da ya faru da ɗiyar Buba Galadima ta kira Tinubu a wayar salula

Asali: Facebook
Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar AIT da aka wallafa a shafin Facebook, inda ya ce matsayinsa a siyasance ya sauya ne saboda yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya so Tinubu ya kori Buba Galadima
A cewar Galadima, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa sabon kwamiti a lokacin da Bola Tinubu ke matsayin jagoran jam’iyyar APC, domin a fitar da shi daga kwamitin amintattu na jam’iyyar.
Ya ce:
“Lokacin da Buhari ya gan ni a cikin kwamitin, sai ya ce bai kamata a rika ganina a can ba, saboda haka sai ya kafa wani kwamitin ƙasa.
Ya nada Bola Tinubu a matsayin shugaban wannan kwamiti — a lokacin yana matsayin jagoran jam’iyyar. Tinubu ya fahimci abin da Buhari ke ƙoƙarin yi.
Kuma har yanzu da nake magana da kai, wannan kwamiti bai zauna ba, bai mika wani rahoto ba, kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar bai canza ba.”
Buba Galadima: ‘Dalilin Buhari na kin Tinubu’
Buba Galadima ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya fusata sosai saboda Tinubu bai aiwatar da umarninsa na cire shi daga kwamitin ba.
Wannan, a cewarsa, yana daga cikin dalilan da suka sa Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba.
Ya ce:
“Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa Buhari bai taba son Tinubu ya zama shugaban kasa ba — saboda ya ƙi cire ni daga kwamitin. Shi yasa na bar jam’iyya. To, yanzu kana ganin zan iya komawa APC? Ka yi tunani da kanka.”

Asali: Facebook
Buba Galadima ya kara da cewa ko da Tinubu bai fito fili ya ce komai ba, amma yana sane da yadda Muhammadu Buhari ke jin haushi da bakin ciki kan yadda ya zama shugaban kasa.
Buba Galadima ya fadi alakarsa da Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa kusa a NNPP Buba Galadima, ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaka da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, duk da kasancewarsa a jam’iyyar adawa.
A cewar Galadima, ɗaya daga cikin ’ya’yansa ta tuntubi shugaban kasa ta hanyar kiran sa a wayar salula domin neman taimako, inda ta koka kan rashin aikin yi bayan ta kammala NYSC.
Ya bayyana cewa nan take, shugaban kasa ya kira shugaban hukumar da ke kula da harkokin man fetur, wato NUPRC, Injiniya Gbenga Komolafe, ya kuma umarce sa ya ba diyarsa aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng