ECONEC: Bayan Labarin Tinubu Ya Tsige Shi, Shugaban INEC Ya Bar Najeriya
- Shugaban Hukumar Zabe ta INEC, Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa zai bar aiki a karshen shekarar da ake ciki
- Ya sanar da haka ne a taron Cibiyar hukumomin zabe na ECOWAS (ECONEC), inda ya shaida cewa wa'adinsa ya kare a INEC
- Mahmood Yakubu ya yi karin hasken ne a lokacin da ake rade radin cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya tsige shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmud Yakubu, ya yi kira da a samu hadin kai mai karfi tsakanin hukumomin zabe na kasashen da ke yankin yammacin Afirka.
Shugaban hukumar ya yi wannan kiran ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron gaggawa na taron majalisar gudanarwar Cibiyar hukumomin zabe na ECOWAS (ECONEC) da aka gudanar a Banjul, Gambia.

Asali: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa, Mahmood Yakubu wanda a baya ya jagoranci kwamitin shugabanci na ECONEC, ya gode wa abokan aikinsa saboda goyon bayan da suka ba shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ya yaba da shugabannin yanzu na ECONEC bisa ci gaba da tabbatar da cewa cibiyar tana aiki kuma tana da muhimmanci.
Shugaban INEC ya yi jawabi a ECONEC
The Guardian ta wallafa cewa shugaban INEC, Mahmud Yakubu ya kuma yabawa jami'an cibiyar da suka gabata wanda suka taka rawa wajen karfafa dimokiradiyya a kasashensu da kuma a nahiyar Afrika.
Sai dai shugaban ya yi nuni da cewa, wasu kasashe guda hudu a yankin sun samu koma baya daga mulkin dimokiradiyya tun daga taron ECONEC na shekarar 2017 da aka yi a Sierra Leone.

Asali: Twitter
Shugaban ya bukaci abokan aikinsa da su tabbatar da ingancin zabubbuka domin inganta tsarin mulki a kasashensu.
Sannan ya shaida wa majalisar cewa wannan shi ne taron ECONEC na karshe da zai halarta a matsayin shugaban INEC, domin karshen wa'adinsa zai kasance daga baya a shekarar nan.
Muhimmancin ECONEC ga kasashen Afrika
Taron ya hada shugabanni da mataimakan shugabanni daga kasashe 11 na yammacin Afirka, ciki har da Najeriya.
Sannan a yayin taron na bana, an yi duba duba da kuma amincewa da sabon tsari na doka da aka sabunta na ECONEC.
Daya daga cikin muhimman kudirori da aka sanya a kan jawalin taron sun hada da kafa dakin bayanai na raba batutuwan zabe na farko a Afirka.
Ana sa ran wannan abu da aka cimma zai taimaka wajen inganta hadin kai da gina ingantaccen tsari kuma karfi a duk fadin nahiyar.
A lokacin ziyararsa a Banjul, shugaban INEC zai hadu da shugaban ECONEC, Konneh Mohamed Kenewui daga Sierra Leone, domin ganawa da wasu muhimman masu ruwa da tsaki.
Sauran wadanda zai gana da su sun hada da jami'an gwamnatin Gambia, domin gudanar da binciken bukatun kasa a gabannin zaben shugaban kasa na shekarar 2026.
Shugaban INEC ya gana da ma'aikatansa

Kara karanta wannan
Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya jagoranci taron mako-mako na hukumar a Abuja, kasa da awanni 24 bayan yada jita-jitar cewa an tsige shi.
A ranar Litinin da ta gabata ne, wani saƙo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda ke bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya maye grubinsa da Farfesa Bashiru Olamilekan.
Mai magana da yawun INEC, Rotimi Oyekanmi, ya karyata labarin, yana mai cewa ba gaskiya ba ne, tare da shawartar jama'a da su yi watsi da batun da ake yada wa don tada tarzoma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng