Tinubu Ya Waiwayi Shugaban Jam'iyyar APC, Ya ba Shi Shirgegen Mukamin Gwamnati

Tinubu Ya Waiwayi Shugaban Jam'iyyar APC, Ya ba Shi Shirgegen Mukamin Gwamnati

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Basil Ejidike, shugaban APC na Anambra, a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta cibiyar NRCRI
  • A cikin wata wasika, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayyana cewa nadin Ejidike ya fara aiki ne tun daga ranar 26 ga Maris
  • Chief Ejidike ya gode wa Tinubu bisa wannan nadi, yana mai cewa hakan ya kara nuna kaunarsa ga APC da mutanen jihar Anambra

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje shugaban jam’iyyar APC na jihar Anambra da baban mukami a gwamnatin tarayya.

Shugaba Tinubu ya nada Chief Basil Ejidike, a matsayin shugaban hukumar gudanarwar cibiyar binciken tsirrai masu jijiyoyi da ke Umudike.

Fadar shugaban kasa ta yi magana da Tinubu ya nada shugaban hukumar gudanarwar NRCRI
Tinubu ya nada shugaban APC na Anambra a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NRCRI. Hoto: Anambra APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya ba shugaban APC mukami

Jaridar Punch ta rahoto cewa an samu bayanin nadin da Shugaba Tinubu ya yi wa Chief Basil ne a cikin wata wasika da saataren gwamnatin tarayya, George Akume ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

'Mun yi kuskure,' Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri kan maganar nada mukamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya nuna cewa Akume ya sanya wa wasikar nadin hannu a ranar 28 ga Maris, 2025, kuma ya ce nadin wani kira ne da aka yi wa Chief Basil domin ya yi wa kasa hidima.

Wasikar ta nuna cewa nadin Chief Basil Ejidike, da aka yi ya fara aiki ne tun daga ranar 26 ga Maris, 2025.

Dalilin Tinubu na ba shugaban APC mukami

Wasikar mai taken “nadin shugaban hukumar gudanarwar cibiyar binciken tsirrai masu jijiyoyi da ke Umudike,” ta bayyana cewa:

"Ina farin cikin sanar da kai cewa mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadinka a matsayin shugaban hukumar gudanarwar cibiyar binciken tsirrai masu jijiyoyi da ke Umudike
"Nadinka, wanda kira ne yi wa kasa hidima, ya nuna irin yardar da shugaban kasa ya dora a kanka na jagorantar wannan babbar cibiya.
"Kuma nadin naka zai fara aiki daga ranar 26 ga Maris, 2025. Ina taya ka murnakuma ina yi maka fatan alheri a sabon aikin da za ka fara.”

Kara karanta wannan

Ana rade radin Tinubu ya tsige shi, Mahmud Yakubu ya saka labule da ma'aikatan INEC

Shugaban APC ya yi wa Tinubu godiya

Shugaban APC ya yi wa Tinubu godiya kan nadin da ya yi masa
Shugaban APC na Anambra ya godewa Tinubu kan ba shi mukami a NRCRI. Hoto: Anambra APC
Asali: Facebook

Ejidike ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa wannan karin girma da aka yi masa da kuma jam’iyyar APC ta jihar Anambra, yana mai cewa nadin ya kara wa jihar daraja, inji Vanguard.

Ya bayyana nadin a matsayin wani karin girmamawa daga shugaban kasa ga Anambra da jam’iyyar APC, alamar godiya ga kokarin ‘ya’yan jam’iyyar da mutanen jihar.

Ejidike ya tabbatar wa shugaban kasa da ci gaba da samun goyon bayan jama’ar jihar da reshen jam’iyyar APC na Anambra, musamman ga manufarsa ta Renewed Hope Agenda.

An taba dakatar da Ejidike daga shugaban APC

Tun da fari, mun taba ruwaito cewa, jamiyyar APC a jihar Anambra ta dakatar da shugabanta, Chief Basil Ejidike, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta dakatar da Chief Basil Ejidike ne bisa zargin saba umurni da kuma rashin kunya ga ofishin shugaban kasa (na lokacin), Muhammadu Buhari.

Sabon shugaban rikon kwarya da aka nada wa jam'iyyar, Okonkwo Okom, ya bayyana cewa an yanke shawarar dakatar da Cif Basil ne a taron shugabanni da masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.