Gaskiya Ta Fito: An Gano Asalin Abin da Ya Kai Gwamnonin APC Wurin Buhari a Kaduna

Gaskiya Ta Fito: An Gano Asalin Abin da Ya Kai Gwamnonin APC Wurin Buhari a Kaduna

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun miƙa ƙoƙon bararsu ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna
  • Tawagar gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Hope Uzodimma ta buƙaci Buhari ya sanya baki a shirin da wasu ke yi na ficewa daga APC
  • Gwamnonin jihohi sun kira sunayen tsofaffin ministoci guda biyu da suke so Buhari ya hana ficewa daga jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Bayanai na fitowa kan ziyarar da wasu gwamnonin jam’iyyar APC suka kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna a ranar Litinin.

Tawagar ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, sun sanya labule da tsohon shugaban ƙasan, suka yaba masa bisa irin nasarorin da ya samu yayin da yake mulki.

Buhari da gwamnonin APC
Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce gwamnonin na APC sun jaddada cewa gwamnatin Buhari ta gina tubalin ci gaba mai ƙarfi ga makomar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari yayin da ake rubibin sauya sheka zuwa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko da yake an bayyana ziyarar a fili a matsayin gaisuwar Sallah, majiyoyi sun bayyana cewa akwai batun siyasa a ziyarar.

Meyasa gwamnonin APC suka ziyarci Buhari

Majiyoyin sun bayyana cewa babban dalilin ziyarar shi ne neman Buhari ya shiga tsakani don daƙile ficewar na kusa da shi daga APC zuwa jam’iyyar SDP.

Rahotanni sun ce koke-koken gwamnonin ya samo asali ne daga ƙaruwar jita-jitar ficewar jiga-jigai daga APC yayin da ake shirin zabukan 2027.

Tsohuwar jam’iyyar CPC da ta narke cikin APC, har yanzu na da ƙarfi sosai, kuma Buhari shi ne ke wakiltar ginshiƙinta.

Akwai fargaba a cikin APC cewa idan ƴan tsagin CPC suka fice, hakan zai iya jefa jam’iyyar cikin rikici a faɗin ƙasar nan.

Taron ya zo ne a daidai lokacin da wasu aminan Buhari ke ficewa daga APC zuwa SDP.

Majiyar da ta samu halartar taron sirrin kuma ta nemi a ɓoye sunanta, ta bayyana cewa gwamnonin sun roƙi Buhari ya yi magana da tsofaffin ministocinsa guda biyu.

Kara karanta wannan

Anambra: Rigima ta ƙara tsanani a APC, ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyya

Majiyar ta ce gwamnonin sun buƙaci Buhari ya yi magana da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, SAN da tsohon ministan ƙaramin ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba, kan ka da su bar jam’iyyar APC.

Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari
Gwamnonin APC sun nemi alfarma wajen Buhari Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Buhari ya ƙi amsa tayin gwamnonin APC

Sai dai, majiyar ta bayyana cewa Buhari ya nuna cewa ba zai tsoma baki ba, yana mai cewa mutane irin su Hon. Nwajiuba da sauransu, su ne za su yanke hukunci kan inda za su tsaya a siyasance.

Sai dai wannan matsayi da Buhari ya ɗauka ya ƙara haifar da jita-jita kan yiwuwar ficewar wasu manyan jiga-jigan APC da kuma illar hakan ga makomar jam’iyyar.

Ficewar mutane irin su Nwajiuba da Malami na iya raunana APC, musamman idan suka sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, shi ya sa gwamnonin suka gaggauta kai ziyara wajen Buhari don neman mafita.

Buhari ya taya Shugaba Tinubu murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammaɗu Buhari ya aika saƙon taya murna ga Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP? An samu bayanai

Tsohon shugaban ƙasan ya aika saƙon ne domin taya mai girma Bola Tinubu murnar cika shekara 73 a duniya.

Muhammadu Buhari ya yi addu'ar Allah ya ba shi lafiya da ƙwarin gwiwar sauke nauyin da ke kansa na shugabantar ƴan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng