Manyan Ƴan Adawa na Shirin Haɗaka, Ɗan Majalisa Ya Sauya Sheƙa zuwa Jam'iyyar PDP
- Jam'iyyar LP ta rasa ɗan Majalisa a jihar Enugu saboda rigingimun cikin gida da suka addabe ta a matakin kasa
- Hon. Eze Gabriel ya bayyana cewa dole ta sa ya yanke shawarar fita daga LP zuwa jam'iyyar PDP domin samun damar ba da gudummuwa
- Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Enugu, Hon. Uche Ugwu ne ya karanta wasiƙar sauya shekar ɗan Majalisar a zaman yau Talata, 8 ga watan Afrilu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Dan majalisar dokokin jihar Enugu, Eze Gabriel, mai wakiltar mazabar Isi-Uzo karkashin jam’iyyar LP, ya sauya sheka zuwa PDP.
Hon. Eze, wanda aka zabe shi a karkashin inuwar LP a zaben 2023, ya bayyana sauya shekar ta sa ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, 8 ga watan Afrilu.

Asali: Facebook
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa kakakin Majalisar Dokokin Jihar Enugi, Hon. Uche Ugwu ne ya karanta wasiƙar sauya shekar a zauren Majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar LP na fama da rikicin shugabanci
Jam'iyyar LP ta rasa ɗan Majalisar ne a daidai lokacin da take fama da rikicin shugabanci bayan hukuncin kotun kolin Najeriya.
LP dai na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa da ake tsammanin za su haɗa ƙa.wance domin kawar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, Atiku Abubakar na PDP da manyan jagororin adawa na shirin haɗewa wuri guda don tunkarar zaɓe na gaba.
Me yasa ɗan Majalisa ya koma PDP?
A wasiƙar da kakakin Majalisar dokokin Enugu ya karanta, Hon Eze ya bayyana damuwa cewa ba a son ransa ya ɗauki matakin barin LP ba.
Ya ce rikicin cikin gida da rabuwar kai tsakanin shugabannin LP na matakin ƙasa da jiha ne suka tilasta shi ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar zuwa PDP.
Ya bayyana cewa LP, wadda a baya take kamar haske ga masu kishin ci gaba, yanzu ta rikide zuwa jam’iyya mai cike da rikici, lamarin da ya sa ta zama duhu mara cika alƙawarin jama'a.

Kara karanta wannan
An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Asali: Twitter
Jam'iyyar LP ta dare gida 2 a matakin ƙasa
Dan majalisar ya ce rikicin da ke tsakanin Julius Abure da Nenadi Usman a matakin kasa, da kuma na Kingsley Ugwu da Casmir Agbo a jihar Enugu, ya kara tabbatar da rashin daidaito a jam’iyyar.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa PDP za ta ba shi damar da ta dace domin ci gaba da bada gudunmawarsa ga ci gaban jihar Enugu.
A ƙarshe, Hon Eze ya gode wa magoya bayansa bisa fahimta da goyon bayan da suke ba shi kan dukkan matakan da ya ɗauka a siyasarsa.
SDP ya roki Obi, Atiku su dawo cikinta
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta yi kira ga manyan yan adawa irinsu Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su taho su haɗa wuri ɗaya.
Mataimakin shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa (Kudu maso Gabas), Sir Arinze Ekelem ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar.
Ekelem ya bayyana cewa jam’iyyar SDP ta samar da sabuwar dama ga ‘yan Najeriya da ke neman sauyi na gaskiya a harkar shugabanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng