Fubara: An Hango Wike na Ganawa da 'Yan Majalisar Rivers a London
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya gana da wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Rivers da aka dakatar, a wata liyafa a Birtaniya
- An ce dakatattun 'yan majalisar suna halartar wani horo na musamman ne a London domin ƙara fahimtar aiki da ƙwarewa a majalisa
- Ganawar 'yan majalisar na zuwa ne a tsakiyar rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Rivers, wanda ya kai ga dakatar da gwamna Simi Fubara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
London - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya karɓi wasu ‘yan majalisar jihar Rivers da ke karkashin jagorancin Martin Amaewhule a wani taron liyafa a kasar Birtaniya.
An shirya taron ne yayin da ‘yan majalisar ke halartar wani horo na musamman a birnin London domin kara ƙwarewa da fahimtar aikin majalisa da kuma inganta tsarin dimokuraɗiyya.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani bidiyo da hadimin Wike, Lere Olayikan ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar ‘yan majalisar na karkashin kulawar Martin Amaewhule, wanda ke jagorantar bangaren majalisar da ke goyon bayan Wike a rikicin siyasar jihar Rivers.
Me ya kai 'yan majalisar Rivers London?
The Cable ta wallafa cewa wata sanarwa daga ofishin mai magana da yawun Amaewhule, Martins Wachukwu, ta ce ‘yan majalisar sun tafi London ne domin halartar wani taro.
A cewar sanarwar, taron na da nufin ba su damar yin nazari da musayar ra’ayoyi tare da wasu ‘yan majalisa daga sassa daban-daban.
Sanarwar ta ce an fara taron ne a tsakiyar birnin London kuma za a shafe kwana biyar ana gudanar da horo da tattaunawa kan dabarun aikin majalisa.
Haka zalika za a horar da su kan karfafa ikon sa ido da tasiri da majalisa ke da shi kan ayyukan gwamnati.
‘Yan majalisar sun bayyana cewa ziyarar na da matukar amfani wajen karawa juna sani da kara wayewa kan yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Makomar ziyarar a siyasar jihar Rivers
Jihar Rivers ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da aka samu sabani tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.
Rikicin ya kai ga rarrabuwar kawuna cikin majalisar jihar, inda kowane bangare ke da nasa shugabanci da goyon baya.
A lokacin rikicin da ya fi muni a shekarar 2023, an yi yunkurin tsige gwamnan wanda hakan ya janyo rusa ginin majalisar jihar.
Ana ganin ganawar da Wike ya yi da 'yan majalisar za ta bude sabon babi kan yadda siyasar jihar Rivers za ta kasance a gaba.

Asali: Facebook
An tarwatsa masu zanga zanga a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a manyan biranen Najeriya ciki har da Fatakwal na jihar Rivers.
Masu zanga zangar sun bayyana cewa sun fito kan tituna ne domin nuna damuwa kan yadda harkokin tattali da siyasa ke dagulewa a Najeriya.
Matasan sun ce rashin tsaro ya karu a Najeriya ga kuma yanayin yadda siyasar jihar Rivers ta rikice har ta kai ga dakatar da gwamna Siminalayi Fubara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng