2027: Makomar Siyasar Saraki a Najeriya da Jita Jitar Komawa Jam'iyyar APC ko SDP

2027: Makomar Siyasar Saraki a Najeriya da Jita Jitar Komawa Jam'iyyar APC ko SDP

  • Yayin da siyasar zaben 2027 ke kara armashi, har yanzu Bukola Saraki bai ce komai ba, duk da yana bangaren 'yan adawa
  • Masu lura da harkokin siyasa sun bayyana mamakinsu kan yadda Saraki bai bayyana cikin tattaunawar hadin gwiwar 'yan adawa
  • Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban majalisar yana yin shiru ne da nufin tsara matakin da zai fi amfani a siyasarsa a 2027
  • Wani na kusa da Saraki ya ce suna iya bin tsarin siyasar Nyesom Wike, inda za su ci gaba da zama PDP amma su yi mu'amala da gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin Kwara - Yayin da siyasar 2027 ke kara tafiya, ana mamakin shiru da Sanata Abubakar Bukola Saraki ke yi har yanzu.

Tun bayan maganarsa kan rikicin Godswill Akpabio da Sanata NatashaAkpoti, bai sake cewa komai ba musamman game da siyasa.

Kara karanta wannan

An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Bukola Saraki ya magantu kan shirin komawa APC
Sanata Bukola Saraki ya na ci gaba da lissafi kan makomar siyasarsa a 2027. Hoto: Abubakar Bukola Saraki.
Asali: Facebook

Menene gaskiyar shirin komawar Saraki APC?

Daily Trust ta ce masu lura da harkokin siyasa sun ce abin mamaki ne ganin Saraki, shahararren dan siyasa, bai shiga tattaunawar hadin kai da Atiku da wasu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan faduwa zabe a 2019 da 2023, tasirin Bukola Saraki a Kwara da Najeriya ya ragu, sai dai wasu na ganin shiru ne na dabara.

A kwanakin baya, Saraki ya karbi bakuncin wasu tsoffin 'yan majalisar dattawa na zango na takwas a gidansa da ke Ilorin domin tattaunawa ta sirri.

Majiyoyi sun bayyana cewa Saraki ya musanta zancen komawa APC, yana cewa maganar karya ce da wasu 'yan APC ke yadawa.

Majiyar ta kara da cewa Saraki bai yarda da yiwuwar kafa sabuwar jam'iyya ba kafin zaben 2027 saboda matsalolin da ke tattare da hakan.

Saraki ya musanta labarin komawa APC ko SDP a Najeriya
An gano yadda Sanata Bukola Saraki ke tsara tafiyarsa a siyasa kafin zaben 2027. Hoto: Abubakar Bukola Saraki.
Asali: Facebook

Dabarun siyasar Bukola Saraki kafin zaben 2027

Wasu sun ce matsalolin da ke ciki ne yasa Saraki bai gaggauta bayyana kansa cikin tattaunawar hadin gwiwa ba.

Kara karanta wannan

'Masarauta ta girmi haka': Shehu Sani kan gayyatar Sarki Sanusi II, ya nemo mafita

Wani na kusa da Sanata Saraki ya ce akwai yiwuwar Saraki zai bi tsarin Nyesom Wike, inda zai ci gaba da zama PDP amma ya hada kai da gwamnati.

Ya ce babu shirin Saraki na komawa SDP, sai dai komai na iya sauyawa gwargwadon yadda siyasa ke tafiya kafin lokacin zaben 2027.

Na hannun daman Saraki ya ce tsohon gwamnan bai da niyyar neman wani mukami yanzu, yana mai mai da hankali kan siyasarsa ta Kwara da kasa baki daya.

Ya kara da cewa shiru da Saraki ke yi dabararsa ce, yana kallon komai, yana lissafi kafin ya yanke hukunci.

Saraki ya soki sabon kudirin harajin Tinubu

Kun ji cewa kungiyar NECA da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun soki sabon harajin kashi 4% da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ƙara.

NECA ta bayyana cewa sabon harajin zai ƙara dagula tattalin arzikin ƙasa, wanda ya riga ya kasance cikin matsala a halin da ake ciki a yanzu.

Saraki ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba lamarin, yana mai cewa harajin zai haifar da tashin farashin kaya da kuma matsin lamba ga 'yan kasuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng