An Bayyana Shirin Atiku da Obi na Haduwa da El Rufa'i a SDP domin Kifar da Tinubu
- 'Dan takarar shugaban kasa a SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce manyan 'yan siyasa kamar Atiku Abubakar da Peter Obi na tattaunawa domin sauya sheka
- Adebayo ya ce wakilan Atiku da Obi na kokarin shirya musu hanya don shiga SDP, bayan ta karbi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai daga APC
- A cewarsa, jam’iyyar SDP ta bude kofofinta ga dukkan masu kishin kasa, tare da shirin karbar dukkan manyan 'yan siyasar da ke da niyyar bin doka da tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayanai na kara fitowa kan shirin hadakar 'yan adawa a Najeriya domin tunkarar jam'iyyar APC a 2027.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo ya ce akwai bayanai da suke samu na cewa Atiku Abubakar da Peter Obi ba shirin shiga jam'iyyar.

Asali: Facebook
Adewole Adebayo ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi a tashar Channels TV, a shirin Sunday Politics.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
"Mutane na shiga jam’iyyarmu, kuma muna karbarsu hannu bibbiyu. Kamar yadda ku ke gani, ina ta aiki wajen maraba da su."
Ya kara da cewa wasu daga cikinsu na amfani da dabarun bayan fage domin ganin sun shiga jam'iyyar SDP.
A kan maganar shigar Peter Obi SDP, Adebayo ya ce:
"Kawai dai har sai mutum ya shigo za mu bayyana wa duniya. Amma mutane da dama sun shaida mani hakan, ciki har da babban ma’ajin jam’iyya."
Ya ce idan dukkan ‘yan siyasar suka bi dokokin SDP da yadda jam’iyyar ke tafiyar da harkokinta, za a iya kafa sabuwar tafiyar da za ta kayar da APC a gaba.
"Za mu karbi kowa cikin mutunci" – SDP
Adewole Adebayo ya jaddada cewa, SDP na karbar duk wanda ke da niyyar canji da biyayya ga doka.
Ya ce jam’iyyar ba za ta yarda da makircin siyasa ko magudi ba, kamar yadda aka gudanar da taronta na 2022 cikin gaskiya da lumana.
"Ina fata za mu hada karfi daya" – Adebayo
Adebayo ya ce yana da tabbas cewa idan suka hada karfi da karfe za su iya kayar da jam'iyyar APC a 2027.
A cewarsa:
"Idan mu ka hada karfi daya, muka zabi shugaba cikin gaskiya da bin doka, za mu kayar da APC kuma mu tura Tinubu Lagos ko inda ya ga dama a Najeriya."
Ya jaddada cewa SDP na da tsari mai kyau, kuma tana da niyyar zama madaidaiciyar hanya ga 'yan Najeriya.

Asali: Facebook
NNPP: Tsagin Kwankwaso ya samu koma baya
A wani rahoton, kun ji cewa kotun tarayya ya yanke matsaya kan karar da tsagin NNPP mai biyayya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigar.
A yayin zaman shari'ar, alkalin kotun ya yi watsi da karar inda ya ce kotu ba ta da hurumin shiga rikicin jam'iyyu na cikin gida.
A karkashin haka ne tsagin Kwankwaso ya nuna rashin jin dadi kan matakin da kotun ta dauka tare da bayyana cewa nan gaba zai fitar da matsayarsa.
Asali: Legit.ng