Anambra: Rigima Ta Ƙara Tsanani a APC, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

Anambra: Rigima Ta Ƙara Tsanani a APC, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

  • Abubuwa sun kara caɓewa jama'iyyar APC yayin da take shirin gudanar da zaben fitar da ɗan takarar gwamna a jihar Anambra yau Asabar
  • Paul Chukwuma, ɗaya daga cikin masu nemin tikitin APC ya janye daga shiga zaɓen kuma ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar
  • Ɗan siyasar ya zama mutum na biyu da ya janye daga shiga zaɓen fidda gwanin APC bayan tsohon ɗan majalisar tarayya, Chukwuma Umeoji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Paul Chukwuma, daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Anambra a inuwar APC ya fice daga jam'iyyar.

Ɗan takarar ya kuma sanar da janye wa daga zaben fitar da gwani na APC wanda aka shirya gudanarwa yau Asabar, 5 ga watan Afrilu, 2025.

Paul Chukwuma.
Dan takarar gwamna a APC Anambra, Paul Chukwuma, ya fice daga jam’iyya Hoto: Paul Chukwuma
Asali: Facebook

The Cable ta ce Chukwuma ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 2, Umueri, a karamar hukumar Anambra ta Gabas.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu nasara, ya zama ɗan takara a inuwar jam'iyyar APGA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar gwamna ya bar jam'iyyar APC

Duk da cewa bai bayyana dalilan ficewarsa daga jam’iyyar ba, kuma bai fadi matakin siyasa da zai dauka na gaba ba, ya ce har yanzu yana da akidar APC a tare da shi.

Har ila yau ɗan siyasar ya ce yana nan tare da kudirin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na sabunta fatan ƴan Najeriya.

A cikin wasikar, Chukwuma ya rubuta cewa:

"Na rubuta wannan wasika ne domin sanar da ku cewa na fice daga jam'iyyar APC, ina ba ku tabbacin cewa ina tare da akidar kawo ci gaba a ƙoƙarin ceto jihar Anambra.”

Zaben Anambara: Wane hali APC ke ciki?

Chukwuma ya zama ɗan takara na biyu da ya janye daga zaɓen fidda gwanin APC a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Hon. Chukwuma Umeoji, tsohon dan majalisar wakilai, shi ne ɗan takara na farko da ya sanar da janyewarsa a ranar Juma’a, bayan tuntubar magoya bayansa a fadin jihar.

Kara karanta wannan

2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1

Jam’iyyar APC ta tantance mutum bakwai domin shiga zaben fidda gwani. Bayan ficewar Chukwuma da Umeoji, sauran ‘yan takara biyar suka rage, rahoton Vanguard.

Jam'iyyar APC.
APC ta kara rasa ɗan takara 1 kafin zaben fidda gwani a Anambra Hoto: APC
Asali: Getty Images

Ƴan takarar da ke neman tikitin APC

Ƴan takarar sun hada da Nicholas Ukachukwu, tsohon dan majalisar tarayya; Valentine Ozigbo, dan takarar PDP a zaben gwamna na 2021; Obiora Okonkwo, Johnbosco Onunkwo, da Edozie Madu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta tsara gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

APC ta zabi amfani da tsarin zaben deleget domin fitar da dan takara, wanda sakataren jam’iyyar na kasa, Ajibola Basiru, ya ce an yi haka ne domin a tafi da kowa.

APC ta ba gwamna tikitin tazarce a 2027

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC ta bai wa Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba tare da mataimakinsa, Peter Odey, tikitin takarar da za su nemi tazarce a 2027.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, mai magana da yawun APC ya rasu a ƙasar waje

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kuros Riba, Alphonsus Eba, ya ce sun yi haka ne duba da nasarorin da gwamnan ya samu a zangon mulkinsa na farko.

Eba ya jaddada cewa ba wanda aka bai wa tikitin takara sai gwamna da mataimakinsa, saura kuma dole sun fafata a zaben fidda gwani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng