Galadiman Kano: Bayan Korafi, Ganduje Ya Dura a Kano, Ya Wuce Fadar Aminu Ado

Galadiman Kano: Bayan Korafi, Ganduje Ya Dura a Kano, Ya Wuce Fadar Aminu Ado

  • Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya isa Kano a yau Asabar domin jajantawa kan rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • Ganduje ya sauka a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano inda ya samu rakiyar manyan jiga-jigan jam'iyyar APC na reshen jihar Kano
  • Ziyarar tsohon gwamnan jihar ta biyo bayan rasuwar mahaifin Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, wanda shi ne Galadiman Kano
  • Daga filin jirgi, Ganduje ya zarce kai tsaye fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero domin miƙa sakon ta'aziyya ga masarauta da mutanen Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dura a jihar Kano a yau Asabar 5 ga watan Afrilun 2025.

Abdullahi Ganduje ya isa Kano ne domin jaje bayan rasuwar dattijo kuma Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Shugaban jam'iyyar APC ya rasu cikin yanayin ban al'ajabi

Ganduje ya dura a Kano bayan babban rashi da aka yi
Bayan rasuwar Galadiman Kano, Ganduje ya kai ziyarar ta'aziyya. Hoto: Musbahu Abdullahi Emirater.
Asali: Facebook

Ganduje ya isa Kano domin ta'aziyyar Galadima

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wani mai suna Shu'aib Kabir ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar 5 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, an gano Ganduje na saukowa daga cikin jirgi a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Ganduje ya samu rakiyar jiga-jigan jam'iyyar APC domin jajantawa gwamnatin Kano da masarauta da sauran al'umma kan rashin da aka yi.

Sanarwar ta ce:

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.
"Ganduje ya iso Kano ne domin yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifin Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, wato marigayi Abbas Sunusi (Galadiman Kano), dattijo mafi girma a masarautar Kano."
Aminu Ado ya karbi bakuncin Ganduje a fadarsa
Abdullahi Umar Ganduje ya isa fadar Aminu Ado Bayero domin jajanta rasuwar Galadiman Kano. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Aminu Ado ya tarbi Ganduje a fadar Nasarawa

Daga bisani, Ganduje ya wuce kai tsaye fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero domin jajanta masa kan rashin da aka yi.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Shafin Masarautar Kano ta wallafa faifan bidiyo a manhajar Facebook inda Aminu Ado Bayero ya tarbi Ganduje a fadarsa da ke Nasarawa a yau Asabar 5 ga watan Afrilun 2025.

Sanarwar ta ce:

"Ziyarar tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban jamiyyar APC ta kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP domin yi masa ta’aziyyar Galadiman Kano a yau Asabar."

Asalin mafarin rikicin masarautar Kano

Rikicin masarautar Kano ya samo asali ne tun lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2019, Ganduje ya tube Muhammadu Sanusi II daga kujerar Sarkin Kano bisa zargin rashin biyayya da kuma wasu batutuwan shugabanci.

Sai dai mutane da dama sun yi amanna cewa sauke Sanusi ya samo asali ne daga bambancin ra’ayi da suka samu tsakaninsa da Ganduje, musamman bayan Sanusi ya fara sukar gwamnatinsa a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Galadima: Aminu Ado na karbar ta'aziyya a fadarsa, sarakuna, 'yan siyasa na tururuwa

Bayan tube Sanusi, Ganduje ya raba masarautar Kano gida biyar, wanda hakan ya rage karfin masarautar da kuma ikon Sarkin Kano na gaba ɗaya.

Abin da ya biyo bayan raba masarautun Kano

Wannan mataki ya janyo cece-kuce a fadin Najeriya, inda wasu ke ganin hakan cin fuska ne ga al’adun gargajiyar Arewacin Najeriya.

A shekarar 2020, Ganduje ya naɗa Aminu Ado Bayero, ɗan marigayi Sarki Ado Bayero, a matsayin sabon Sarkin Kano na 15.

Wannan ya ƙara rura wutar rikicin, inda magoya bayan tsohon sarki Sanusi da sabuwar masarauta ke ci gaba da samun sabani.

Ko bayan sauyin mulki a 2023, batun masarautar Kano ya ci gaba da kasancewa abin ce-ce-ku-ce a siyasa da al’adun jihar.

Galadiman Kano: Aminu Ado na karɓar jama'a a fada

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na ci gaba da karbar ta’aziyya bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi Bayero.

Kara karanta wannan

Ana zaman makokin Galadiman Kano, mummunar gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero'

Basaraken ya karbi wakilan Sarkin Hadejia, Dr. Adamu Abubakar Maje, da sauran manyan baki a fadarsa ciki har da dattijo kuma ɗan siyasa a Kano, Alhaji Tanko Yakasai.

Ana ta ci gaba da kai ziyarar fadar Nasarawa domin jajanta wa basaraken kan babban rashi da aka yi a Kano da Arewacin Najeriya da dama kasa baki daya.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng