Ta Tabbata Atiku Abubakar Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP? An Samu Bayanai

Ta Tabbata Atiku Abubakar Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP? An Samu Bayanai

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya fice daga jam'iyyar PDP
  • Atiku ya musanta rahotannin inda ya bayyana su a matsayin marasa tushe waɗanda babu ƙamshin gaskiya sam a cikinsu
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar.

Atiku Abubakar ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya marasa tushe da kuma wani yunƙuri na bata masa suna a siyasance.

Atiku ya musanta ficewa daga PDP
Atiku Abubakar ya musanta ficewa daga jam'iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma’a, 4 ga watan Afirilun 2025.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya musanta ficewa daga PDP

Sanarwar na zuwa ne a matsayin martani ga jita-jitar da ta yaɗu sakamakon wani rubutu da aka wallafa a wani shafin Facebook mai suna ‘Adamawa Happenings’.

Wannan rubutu ya zargi Atiku da cewa ya fice daga jam’iyyar PDP, abin da ya tayar da hankulan magoya bayansa da kuma sauran jama'a.

Paul Ibe ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana shi a matsayin mara tushe kuma aikin rashin kunya na siyasa da aka shirya don kawo ruɗani da yaudarar ƴan Najeriya.

“Atiku Abubakar bai, mun maimaita, bai fice daga jam’iyyar PDP ba. Har yanzu mamba ne nagari, sahihi, kuma mai biyayya ga jam’iyyar."

- Paul Ibe

Sanarwar ta bayyana rahoton da aka wallafa a Facebook a matsayin aikin wasu ɓoyayyun ƴan siyasa da ke ƙoƙarin haifar da rigima a cikin jam’iyyar adawa da kuma kawo saɓani a tsakanin masu goyon bayan Atiku.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Dalilin Shugaba Tinubu na korar Mele Kyari daga NNPCL

Atiku ya buƙaci a yi watsi da batun

Sanarwar ta buƙaci ƴan Najeriya da mambobin jam’iyyar da su yi watsi da ƙaryar da aka ƙirƙira da gangan, wadda ba ta da wani sahihin tushe ko hujja.

Atiku Abubakar
Atiku ya musanta barin jam'iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya yi takarar shugabancin ƙasa sau da dama.

Har yanzu yana daga cikin fitattun jiga-jigan jam’iyyar PDP kuma babban murya a siyasar adawa.

Sanarwar ta jaddada cewa har yanzu yana yin cikakkiyar biyayya ga akiɗar jam’iyyar PDP da kuma burin ƴan Najeriya na samum dimokuradiyya mai inganci.

Wannan jita-jitar ta ƙarya kan ficewarsa daga jam’iyyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirin yin haɗaka gabanin babban zaben 2027, wanda ake ganin Atiku na daga cikin manyan ƴan takarar da ake sa ran za su sake jaraba sa'arsu.

Tushen jita-jitar ficewar Atiku Abubakar daga PDP

A 'yan shekarun nan, jita-jita da rahotanni marasa tushe sun yawaita cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya caccaki Tinubu, ya fadi sauyin da zai kawo da shi ne shugaban kasa

Wannan batu ya sake daukar hankali a watan Afrilu 2025 bayan wani rubutu da aka wallafa a dandalin Facebook, inda aka bayyana cewa Atiku ya bar jam’iyyar. Wannan ya haifar da ɗumbin ruɗani tsakanin magoya bayansa da mambobin jam’iyyar.

Sai dai, Atiku ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya karyata wannan zargi, yana mai cewa ƙaryace tsagwaronta da kuma ƙoƙarin bata masa suna ne ta hanyar siyasa.

Sanarwar ta bayyana cewa Atiku har yanzu cikakken mamba ne na PDP, kuma yana biyayya ga tsarin jam’iyyar da burin samar da gaskiya da ingantacciyar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Wannan jita-jitar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashe game da yiwuwar Atiku sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027, wanda hakan ke sanya sunansa ci gaba da kasancewa cikin baki na jama'a a harkar siyasa.

Atiku ya yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi

Kara karanta wannan

APC: Jiga-jigan PDP sun fitar da matsaya kan kawancen jam'iyyu gabanin 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi ta'aziyya kan rasuwar malamin addinin musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz Tushen Tanshi.

Atiku ya nuna jimaminsa kan rasuwar malamin wanda ya bayyana a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilmi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa ba iyalan marigayin kaɗai ba ne suka yi rashinsa.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng