Bayan Nasarar APC a Kotu, Amurka Ta Gargadi Najeriya kan Shari'ar Zaben Edo
- Jakadan Amurka a Najeriya ya jaddada bukatar gaskiya da bin doka a sauraron karar zaben gwamna a jihar Edo
- Rahoton KDI ya nuna kura-kurai masu yawa a wajen tattara sakamakon zabe, musamman a jihohin Edo da Ondo
- Kasar Amurka ta ce za ta ci gaba da sa ido kan yadda za a tafiyar da shari'ar zaben domin adalci da amincewar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ta bukaci da a tabbatar da gaskiya da bin doka a shari’ar karar zaben gwamnan jihar Edo.
Amurka ta ce ta yi magana ne da nufin daukar matakin kare darajar dimokuradiyya da tabbatar da amincewar jama’a da tsarin zabe.

Asali: Facebook
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na ofishin jakadancin Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar na mayar da martani ne ga rahoton zaben gwamna na Edo da Ondo da wata kungiya mai zaman kanta, Kimpact Development Initiative (KDI), ta fitar a shekarar 2024.
Zaben Edo: Amurka na son a yi adalci a kotu
Jakadan Amurka ya bayyana cewa gaskiya da bin doka na da muhimmanci wajen tabbatar da sahihancin tsarin dimokuradiyya.
Ya kara da cewa Amurka na goyon bayan zabe nagari kuma za ta ci gaba da lura da yadda za a tafiyar da karar zaben Edo.
A cewarsa:
“Muna bibiyar shari'ar, musamman ganin yadda kungiyoyin fararen hula suka nuna damuwa kan kura-kurai da aka samu a wajen tattara sakamakon zaben.”
Mills ya ce Amurka za ta tsaya tsayin daka wajen ganin cewa Najeriya ta ci gaba da gudanar da sahihan zabuka.
Rahoton KDI ya fallasa kura-kuran zabe
Tribune ta wallafa cewa rahoton da KDI ta fitar ya mayar da hankali kan yadda aka tattara sakamako, bin tsari wajen isar da bayanai da kuma sahihancin tsarin zaben.

Kara karanta wannan
"Na ɗauki laifin," Gwamna ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan abin da ya faru a gadar sama
An gudanar da binciken ne daga rumfunan zabe, cibiyoyin tattara sakamako da kuma shafin IReV na INEC, inda aka gano matsaloli da dama da ke bukatar gyara a tsarin zabe.
Binciken ya nuna cewa akwai sabani a lambobin masu kada kuri’a a rumfunan Edo guda 141 da na Ondo guda 87.
Matsalolin da aka samu a zaben Ondo
Ko da yake jihar Ondo ta samu ci gaba idan aka kwatanta da zaben 2020, inda ta rage kurakurai da kashi 41%, amma hakan bai hana samun kurakurai ba.
A cewar rahoton, Edo ta samu gibin masu kada kuri’a har 18,340 yayin da Ondo ta samu 1,926, abin da ke nuna bukatar sake duba tsarin INEC.

Asali: Facebook
Rahoton ya ba da shawarar a aiwatar da gyare-gyare domin karfafa tsarin zabe da tabbatar da adalci a gaba.
An gargadi Tinubu kan tafiya Faransa
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP ya soki Bola Ahmed Tinubu kan tafiya kasar Faransa.
Bode George ya ce bai kamata Bola Tinubu ya tafi Faransa hutu ba alhali Najeriya na cikin matsaloli da dama.
A cikin kalaman da ya yi, Bode George ya ce ana fama da matsalolin siyasa kamar na Rivers da Sanata Natasha Akpoti a Kogi, ga rikicin Edo amma Bola Tinubu ya tsallake ketare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng