'Kotu Ta Kori Kwankwasiyya?' Jam'iyyar NNPP Ta Fayyace Hukuncin Kotu

'Kotu Ta Kori Kwankwasiyya?' Jam'iyyar NNPP Ta Fayyace Hukuncin Kotu

  • Jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Ahmed Ajuji ta musanta cewa kotu ta dawo da tsagin Agbo Major, kamar yadda wasu ke yadawa
  • Sakataren yada labaran jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce kotu ba ta yi hukunci a kan batun tsagin Major ba, domin ba ta da hurumi
  • Alƙali M.A. Hassan ya yanke hukunci cewa kotu ba ta da wani hurumi na sauraron rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ajuji Ahmed, ta bayyana cewa kotu ba ta dawo da tsagin Agbo Major ba, kamar yadda wasu ke yadawa.

Tsagin Ahmed yana da alaka da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da tsagin Major ke goyon bayan Boniface Aniebonam, wanda ya kafa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Kwankwaso
NNPP ta musanta ikirarin tsagin Major Agbor Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

A wani sako da aka wallafa a shafin Facebook na Sakataren yada labaran jam'iyyar, Ladipo Johnson, NNPP ta ce tsagin Agbo Major yana ƙirƙirar ƙarya dangane da hukuncin kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Koken da tsagin NNPP ya shigar kotu

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ahmed da wasu mutane 20 sun shigar da ƙara gaban kotu domin soke taron jam’iyyar da ya haifar da zaɓen Major a matsayin shugabanta da sauran 'yan kwamitin.

Masu ƙarar sun roƙi kotu da ta hana shugabannin da 'yan kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar gudanar da taruka ko jagorantar babban taron jam’iyyar NNPP na ƙasa.

Hukuncin kotu kan tsagin jam'iyyar NNPP

Alƙali M.A. Hassan, wanda ya jagoranci sauraron ƙarar, ya yanke hukunci cewa kotu ba ta da hurumin sauraron irin wannan ƙara.

Ya kara da jaddada cewa rikice-rikicen da suka shafi shugabancin jam’iyya da 'ya'yanta ba sa ƙarƙashin ikon shari’a.

Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

A cewar hukuncin kotu:

Kara karanta wannan

'Ana neman a sanya dokar ta baci a Edo kan kisan Hausawa,' Jam'iyyar APC

“Matsayar doka, kamar yadda kotun ɗaukaka ƙara da kotun koli suka tabbatar, a bayyane take: Kotuna ba sa yin shari’a a kan abubuwan da suka shafi harkokin cikin gida na jam’iyya, sai dai idan lamarin ya shafi tsaftacewa ko zaɓen ’yan takara kawai.”

Da yake magana da ’yan jarida bayan hukuncin, lauya mai kare masu ƙara, Segun Fiki, ya bayyana cewa hukuncin ya amince da Major da Aniebonam a matsayin sahihin shugabancin jam’iyyar.

Jam'iyyar NNPP ta yi fatali da ikirarin Agbor

Ladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na tsagin Ahmed a NNPP, ya ce kotu ba ta dawo da tsagin Major ko shugabancin sa ba.

A cewarsa:

“Kotun mai girma ba ta yi wani bayani game da sahihancin ƙarar da ke gabanta ba, kamar yadda ya dace, domin ta ce ba ta da hurumi a kai."
“Kamar yadda aka zata, wasu daga cikin waɗanda ake ƙara a shari’ar – waɗanda har yanzu suna cikin korarrun jam’iyyar – sun hanzarta yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar gurbata ma’anar hukuncin.”

Kara karanta wannan

APC: Jiga-jigan PDP sun fitar da matsaya kan kawancen jam'iyyu gabanin 2027

“Ba kamar ƙaryar da suke yadawa ba, babu wata sanarwa daga kotu da ta ba da sahihanci ko iko ga kowace irin kwamitin amintattu. Kotu ta ƙi karɓar shari’ar ne saboda lamarin na cikin gida ne na jam’iyyar.”

NNPP ta ce saboda haka, korar Boniface Aniebonam da abokan tafiyarsa tana nan daram, kuma hukuncin kotu bai taɓa wannan batu ba.

Kotu: Tsagin NNPP na ikirarin nasara

A baya, mun wallafa cewa tsagin NNPP karkashin Dr. Boniface Aniebonam da Dr. Agbo Major ta bayyana cewa kotu ta tabbatar mata da nasara a kotu ta hanyar korar magoya bayan Kwankwaso.

Kotu ta watsi da karar da tsagin Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigar, tana mai cewa batutuwan shugabanci a cikin jam’iyya ba su cikin ikon shari’a, illa idan batun ya shafi takarar zabe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng