Kotu Ta Tabbatar Kwace Shugabancin NNPP daga Tsagin Kwankwaso
- Kotun Babban Birnin Tarayya ta yi watsi da karar da bangaren Sanata Rabiu Kwankwaso ya shigar kan shugabancin jam’iyyar NNPP
- Alkali ya ce kotu ba ta da hurumin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na jam’iyya, sai dai a batutuwan takarar zabe da sauransu
- Bangaren Kwankwaso ya bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin, yana mai cewa za su fitar da cikakken bayani nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi fatali da karar da wasu magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka shigar.
Sun shigar da karar ne suna kalubalantar halaccin shugabancin jam’iyyar NNPP karkashin Dr Boniface Aniebonam da Dr Agbo Major.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa kotun ta yi watsi da karar, tana mai cewa batutuwan shugabanci a cikin jam’iyya ba su cikin ikon shari’a, illa idan batun takarar zabe ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu karar da suka hada da Dr Ahmed Ajuji da wasu mutum 20, sun bukaci kotu ta hana shugabannin NNPP gudanar da taruka, shirya gangami da kuma jagorantar taron jam’iyyar.
Matakin kotu kan shugabancin NNPP
Alkalin kotun, M.A. Hassan, ya yanke hukunci da cewa babu hurumin kotu a irin lamarin, yana mai cewa shari’o’in da suka shafi shugabancin jam’iyya na cikin harkokin cikin gida.
“Doka ta bayyana cewa kotuna ba sa tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyya, sai dai a batutuwan da suka shafi tsaida ‘yan takara don shiga zabe,”
- M.A Hassan
Da wannan hukuncin, kotun ta yi fatali da duk bukatun masu karar, lamarin da ke tabbatar da cewa bangaren Agbo Major ne ke da ikon shugabantar jam’iyyar.
Kotu ta jaddada hukuncin da aka yi a Abia
Wannan hukunci ya jaddada matakin da wata kotu a jihar Abia ta dauka a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan
'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo
A wancan zaman, kotun jihar Abia ta tabbatar da cewa kwamitin amintattun jam’iyyar karkashin Dr Boniface Aniebonam ne ke da cikakken iko.
Lauyan wadanda aka shigar da kara, Segun Fiki, ya yaba da hukuncin, yana mai cewa hakan ya tabbatar da sahihancin shugabancin NNPP.
Bangaren Kwankwaso ya nuna rashin jin dadi
A nasa bangaren, kakakin yada labarai na bangaren Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya bayyana rashin jin dadinsu kan hukuncin, yana mai cewa babu adalci a cikin shi.
“Alkali ya ce wannan lamari ne na cikin gida na jam’iyya, amma hakan ba yana nufin an tabbatar da halaccin Agbo Major ba ne.
"Wannan wata dabara ce kawai don karkatar da hankulan jama’a,”
- Ladipo Johnson
Ya kara da cewa bangarensu zai fitar da sanarwa nan gaba domin fayyace matsayinsu kan hukuncin.

Asali: Facebook
Kwankwaso ya karbi 'yan APC zuwa PDP
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya karbi wasu 'yan jam'iyyar APC da suka sauya sheka a jihar Kano.
Kwankwaso ya karbi mutanen ne yayin da ake bikin sallah bayan kammala azumin watan Ramadan na 2025.
Bayan karbar mutanen, tarin magoya bayan Kwankwasiyya sun kai wa Rabiu Kwankwaso gaisuwar sallah kamar yadda suka saba duk shekara.
Asali: Legit.ng