"Wa'adinka Ya Ƙare," Kotun Kolin Najeriya Ta Tsige Shugaban Jam'iyya na Ƙasa

"Wa'adinka Ya Ƙare," Kotun Kolin Najeriya Ta Tsige Shugaban Jam'iyya na Ƙasa

  • Kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta warware rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar LP ta ƙasa na tsawon lokaci
  • A ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilu, 2025, kotun koli ta tunɓuke Julius Abure daga matsayin shugaban LP, ta ce wa'adinsa ya riga ya ƙare
  • Kotun ta kuma soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, tana mai bayyana cewa ba ta da hurumin yin katsalandan a harkokin jam'iyyar siyasa na cikin gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta kawo karshen taƙaddama kan shugabancin ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa watau LP da aka jima ana rigima a kai.

A yau Juma'a, 4 ga watan Afrilu, 2025, Kotun Koli ta Najeriya, ta yanke hukuncin tsige Julius Abure daga matsayin Shugaban Jam’iyyar LP na kasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta tabbatar da kwace shugabancin NNPP daga tsagin Kwankwaso

Julius Abure.
Kotun Kolin Najeriya ta sauke Abure daga kujerar shugabancin jam'iyyar LP na kasa Hoto: @NGLabour
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa kwamitin alkalai biyar na kotun mai daraja ta ɗaya ne suka yanke wannan hukunci kan karar da aka ɗaukaka zuwa gabansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun koli ta tsige shugaban LP na ƙasa

A hukuncin da kwamitin alkalai ya yanke a dunkule, kotun ta rushe hukuncin Kotun Daukaka Kara da ke Abuja, wacce ta amince da Abure a matsayin shugaban LP.

Kotun ta bayyana cewa Kotun Daukaka Kara ba ta da hurumin yanke hukunci a kan batun shugabancin jam’iyya, domin lamari ne da ya hafi harkokin cikin gida.

Kotun Koli ta kuma ƙara da cewa karar da Sanata Esther Usman da wani mutum guda suka ɗaukaka har zuwa gabanta tana da inganci.

A don haka ta amince da karar, tana mai cewa matakin da Kotun Daukaka Kara ta dauka ya sabawa doka domin ba ta hurumin tsoma baki a harkokin cikin gida na jam'iyyun siyasa.

Wa'adin Abure a shugabancin LP ya kare

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Bugu da kari, Kotun Koli ta lura cewa wa’adin shugabancin Abure a jam’iyyar LP ya riga ya kare, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

"Saboda haka, ba shi da wani ingantaccen dalili na ci gaba da rike mukamin shugaban jam’iyyar," in ji kotun.

Sakamakon haka, kotun ta yi watsi da ƙorafin da bangaren Abure ya shigar, tana mai bayyana cewa ba za a iya dawo da shi kan kujerar shugabancin jam’iyyar ba.

Abure.
Kotun koli ta kawo ƙarshen rikicin shugabancin LP Hoto: @NGLabour
Asali: Twitter

Kotu ta warware rikicin jam'iyyar LP

Wannan hukunci ya kawo karshen rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar LP na tsawon lokaci, inda bangarori daban-daban ke takaddama kan halaccin shugabancin Abure.

Hukuncin Kotun Koli yana nufin cewa jam’iyyar LP na da dama da ikon ta zaɓi sabon shugaba bisa tanadin kundin tsarin mulkinta.

Tuni magoya bayan bangarorin jam’iyyar suka fara mayar da martani kan hukuncin, inda wasu ke yabawa da matakin kotu, yayin da wasu ke kokawa da hukuncin.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da shugaban Majalisa matakin da ta ɗauka kan buƙatar tsige Sanata Natasha

Ɗan takarar LP a 2023 ya koma PDP

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar LP ta gamu da koma baya da tsohon ɗan takararta na gwamna a jihar Enugu ya sauya sheƙa zuwa PDP.

Cif Chijioke Edeoga ya rike muƙamai da dama a inuwar PDP kafin daga bisani ya karɓi tafiyar LP gabanin babban zaɓen 2023.

Bayan komawa PDP a wannan karon, tsohon ɗan Majalisar ya yaba da shugabancin Gwamna Peter Mbah na Enugu, ya ce zai ba da ta sa gudummuwar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng