INEC Ta Sanar da Shugaban Majalisa Matakin da Ta Ɗauka kan Buƙatar Tsige Sanata Natasha

INEC Ta Sanar da Shugaban Majalisa Matakin da Ta Ɗauka kan Buƙatar Tsige Sanata Natasha

  • Hukumar INEC ta sanar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio cewa buƙatar tsige Natasha Akpoti-Uduaghan ba ta cika ƙa'ida ba
  • INEC ta sanar da Akpabio matakin da ta ɗauka ne jim kaɗan bayan ta sanar da jingine kudirin na yi wa sanatar Kogi ta Tsakiya kiranye
  • A cewar INEC, adadin mutanen mazabar Kogi ta Tsakiya da suka rattaɓa hannu z bukatar tsige Natasha ba su kai tanadin kundin tsarin mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, matakin da ta ɗauka kan bukatar korar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Hukumar INEC ta sanar da Sanata Akpabio cewa kudirin tsige sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya bai cika sharuddan da doka ta tanada ba.

Kara karanta wannan

Abin da Sanata Natasha ta ce da INEC ta yanke hukunci kan bukatar kwace kujerarta

Akpabio da Natasha.
Hukumar INEC sanar da Akpabio matakin da ta ɗauka kan tsige Sanata Natasha Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa INEC ta yi fatali da kudirin ne saboda ya gaza cika ƙa'idojin kundin tsarin mulkin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta ɗauki matsaya kan batun Natasha

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025, INEC ta bayyana cewa ta yi nazari kan sa hannun masu bukatar korar sanatar daga mazaɓarta.

Hukumar ta bayyana cewa adadin waɗanda ke bukatar yi wa Sanata Natasha kiranye bai kai yawan waɗanda doka ta gindaya ba.

INEC ta ce bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), a sashe na 69(a), dole ne a samu goyon bayan akalla kashi 50% + 1 na masu katin zabe a mazaɓarta.

A Kogi ta Tsakiya, adadin masu zabe da aka tantance sun kai 474,554, wanda ke nufin ana buƙatar akalla mutum 237,278 su rattaba hannu kan bukatar yi wa ƴar Majalisar kiranye.

Me yasa INEC ta ki yarda da korar Natasha?

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Hukumar INEC ta gama nazarin bukatar tsige Sanata Natasha, ta yi hukunci

Sai dai bayan INEC ta tantance, ta gano cewa mutum 208,132 ne suka sanya hannu kan bukatar, wanda ke nufin kaso 43.86% kacal na masu rajistar zabe a Kogi ta Tsakiya.

Wannan adadi bai kai yawan da ake bukata don aiwatar da tsarin yi wa ƴar Majalisar Dattawan kiranye ba, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Bisa wannan dalilin ne hukumar INEC ta ce ta dakata daga nan, ba za ta ɗauki wani mataki kan wannan lamari ba bisa tanadin sashe na 2(d).

Mahmud Yakubu.
Shugaban Majalisar Dattawa ya samu labarin matakin da INEC ta ɗauka a hukumance Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

INEC ta sanar da Akpabio halin da ake ciki

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta aika da takardar hukuncin da ta yanke zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu manyan ‘yan majalisa.

Sanarwar kuma ta bayyana cewa an wallafa bayanin watsi da buƙatar kiranye a shafukan sada zumunta na hukumar INEC domin ƴan Najeriya su san halin da ake ciki.

Sanata Natasha ta nuna farin cikinta

Kara karanta wannan

Bayan bijirewa gwamnati, Sanata Natasha ta sake dura kan Akpabio da tsohon gwamna

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) ta bayyana farin cikinta da hukumar INEC ta ba masu yunkurin tsige ta kunya.

Sanata Natasha ta ce wannan nasara ce gare ta, ƴan mazaɓarta da ƴan Najeriya gaba ɗaya, tana mai cewa gaskiya ce kawai ta yi halinta.

Natasha ta jinjinawa INEC kan wannan namijin kokarin da ta yi na ganin rashin cancantar bukatar da aka gabatar mata na yi mata kiranye daga majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262