Kurunƙus: Hukumar INEC Ta Gama Nazarin Bukatar Tsige Sanata Natasha, Ta Yi Hukunci

Kurunƙus: Hukumar INEC Ta Gama Nazarin Bukatar Tsige Sanata Natasha, Ta Yi Hukunci

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC ta ce kudirin dawo da sanar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan gida bai cika ƙa'ida ba
  • A wata sanarwa da INEC ta fitar ranar 3 ga watan Afrilu, 2025, ta ce ta gama tantance mutanen mazaɓarta da suka nemi yi wa sanatar kiranye
  • Sai dai hukumar INEC ta ce adadin bai kai wanda sashe na 69(a) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC ta yi watsi da bukatar tsige sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.

Hukumar INEC ta bayyana cewa ƙorafin da mutanen Kogi ta Tsakiya suka shigar na yi wa Sanata Natasha kiranye bai cika ƙa'idar kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

Natasha Akpoti.
Hukumar INEC ta yi fatali da bukatar tsige Sanata Natasha Hoto: Natasha H. Akpoti
Asali: Twitter

Yunkurin yi wa Natasha kiranye bai cika ka'ida ba

Kara karanta wannan

Abin da Sanata Natasha ta ce da INEC ta yanke hukunci kan bukatar kwace kujerarta

INEC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X yau Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Bukatar da aka gabatar don tunbuke sanata mai wakiltar Mazabar Sanatan Kogi ta Tsakiya ba ta cika ka’idojin da sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada ba.

Da take ƙarin bayani, hukumar INEC ta bayyana cewa bisa tsarin doka, dole a samu fiye da rabin masu kaɗa kuri'a a mazaɓar Kogi ta Tsakiya kafin a yi wa Natasha kiraye.

Dalilin INEC na ɗaukar wannan mataki

A cewar INEC, mutanen da suka rattaɓa hannu a ƙorafin tsige sanatar ba su kai adadin da kundim tsarin mulki ya gindaya ba.

"Ƙorafi na kiranye dole ne ya cika sharuddan sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya 1999, wanda ya buƙaci sa hannun fiye da rabin adadin masu rajistar kada kuri’a a mazabar.

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

"Jimillar masu kada kuri’a a Mazabar Kogi Ta Tsakiya, 474,554. Fiye da rabin wannan adadi (wato 50%+1) shi ne 237,277+1 wanda ke nufin akalla 237,278 na masu katin zaɓe.
"Daga cikin rumfunan zabe 902 da ke kananan hukumomi biyar, mun tantance cewa an gabatar da sa hannun mutane 208,132 daga cikin wadanda suka shigar da korafin.

- In ji sanarwar INEC.

A cewar INEC, wannan adadi bai wuce kashi 43.86% na masu katin zaɓe a mazaɓar ba, wanda ya kasa cika sharadin da kundin tsarin mulki ya gindaya.

"Saboda haka, korafin bai cika sharadin sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulki ba. Don haka, ba zai yiwu a yi wa sanatar kiranye ba," in ji sanarwar.

Lauyan Natasha ya zargi gwamnatin Kogi

A wani labarin, kun ji cewa lauyan da ke kare Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya tsoma baki kan yunƙurin da ake yi yi mata kiranye daga majalisar dattawa.

Victor Giwa ya zargi gwamnatin jihar Kogi da ɗaukar nauyin ƙoƙarin raba Sanata Natasha mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya da kujerarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel