Bayan Kisan Ƴan Arewa: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Gwamnan Edo

Bayan Kisan Ƴan Arewa: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Gwamnan Edo

  • Kotun sauraron kararrakin zaɓen Edo ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar AA ta shigar, tana mai cewa an kori karar bisa rashin cancanta
  • Jam'iyyar AA ta zargi INEC da hana sahihin ɗan takararta shiga zaɓe, amma kotun ta ce batun ya wuce huruminta tun da ya faru kafin zaɓe
  • Bayan watsi da ƙarar AA da kuma karar da jam'iyyar AP, an ce kotun za ta koma kan ƙarar PDP da ɗan takararta suka shigar kan zaben

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan Edo da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar AA ta shigar na neman soke zaɓen Gwamna Monday Okpebholo.

Wani kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a Wilfred Kpochi ta yanke hukuncin a ranar Laraba, 2 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Musulmi sun ba Hausawa shawara kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Kotun sauraran kararrakin zaben Edo ta yi hukuncin kan shari'ar neman soke nasarar Gwamna Okpebholo
Kotu ta yi hukunci a karar da jam'iyyar AA ta shigar na neman soke zaben Gwamna Okpebholo. Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Facebook

Kotu ta kori karar neman tsige gwamnan Edo

Mai shari'ar Kpochi ya shaida cewa kotun ta yi watsi da ƙarar da shugaban jam’iyyar AA na ƙasa, Adekunle Rufai Omoaje, ya shigar saboda rashin cancanta, inji Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun sauran kararrakin zaben ta kuma bayyana cewa ƙarar da ta shafi batutuwan da suka faru kafin zaɓen jihar, sun wuce huruminta.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa hukumar zaɓe ta kasa (INEC) ta hana sahihin ɗan takararsu shiga zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba, 2024.

Haka nan sun yi ƙorafi cewa INEC ta yi watsi da hukuncin kotu ta hanyar amincewa da wani ɗan takara da ba jam’iyyar ta tsayar da shi ba.

Hukuncin da kotu ta yanke kan zaben Edo

A hukuncin da ta yanke kan karar da jam'iyyar AP, kotun ta yi watsi da ƙarar soke nasarar Okpebholo bisa rashin cancanta, tana mai cewa masu ƙarar ba su gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin su ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala za ta maka Dan Bello a kotu kan zargin Sheikh Bala Lau

Kotun ta ce masu ƙarar sun yi zargin cewa zaɓen gwamnan Edo na ranar 21 ga Satumba, 2024, yana cika da maguɗi da rashin bin doka.

Sai dai, a cewar kotun, masu ƙarar sun gaza kawo shaidu ko hujjojin da za su tabbatar da zargin cin hanci da rashin bin dokoki a lokacin zaɓe.

Kotun ta ce masu ƙara sun yi “zarge-zarge na gama-gari” amma ba su fadi takamaiman rumfunan zaɓe da gundumomin da ake zargin maguɗin ya faru ba.

Kotun ta bayyana wasu daga cikin zarge-zargen da masu ƙarar suka gabatar a matsayin “marasa tushe” da kuma rashin isassun hujjoji.

Kotu za ta koma zama kan karar da PDP ta shigar

Kotun ta kori karar da jam'iyyun AA da AP suka shigar kan kalubalantar zaben Edo
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo. Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

A baya, INEC ta bayyana cewa Okpebholo na APC ya samu ƙuri’u 291,667, inda ya doke Ighodalo na PDP da ya samu ƙuri’u 247,655.

Kara karanta wannan

Ana shirin haɗaka don kayar da Tinubu, ƴar majalisar tarayya ta fice daga YPP

Ɗan takarar jam’iyyar AP kuwa ya samu ƙuri’u 252 kacal, abin da ya jefa jam’iyyarsa cikin matuƙar rashin jin daɗi.

Jam’iyyar AP da ɗan takararta sun shigar da ƙara suna cewa zaɓen cike yake da maguɗi, cin zarafi, da rashin amfani da BVAS yadda ya kamata.

Kotun karkashin Mai Shari’a Kochi ta yanke hukunci cewa ƙarar ba ta da wata hujja mai ƙarfi da za ta iya tabbatar da maguɗin da ake zargin an aikata.

Yanzu kotun za ta ci gaba da sauraron ƙarar da PDP da ɗan takararta Ighodalo suka shigar suna neman ayyana su a matsayin wadanda suka lashe zaben.

Ya zama ruwan dare kashe mutane a kan hanyoyi, musamman a jihohin Kudancin Najeriya bisa zargin ta'addanci ko nuna kabilanci.

Okpebholo ya dura Kano kan kisan 'yan Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya isa Kano don yi wa Gwamna Abba Kabir da iyalan mutanen 16 da aka kashe a Uromi, jihar Edo, ta'aziyya.

Kara karanta wannan

Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC

Ziyarar ta musamman na nufin nuna alhinin gwamnan kan lamarin da ya faru da mutanen da aka kashe a makon da ya gabata a jiharsa.

Wata sanarwa ta bayyana cewa Okpebholo ya gana da Gwamna Abba Kabir a gidan gwamnati, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan sannan aka raka shi zuwa garin da suke.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng