Zargin Kitsa Kashe Natasha: Akpabio da Gwamna Ododo Sun Yi Magana
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta kai ziyarar sallah mazabarta duk da haramta taruka da gwamnatin Kogi ta yi a ranar Talata
- A yayin taron da aka gudanar, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Gwamna Ahmad Ododo da neman kashe ta
- Biyo bayan maganar da Natasha ta yi, gwamnatin Kogi ta musanta zargin, ta na cewa Sanatar na kokarin tayar da zaune tsaye ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Rikicin siyasa a jihar Kogi ya dauki sabon salo bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ziyarci mazabarta duk da haramta taruka da gwamnati da ‘yan sanda suka yi
Ziyarar da Sanatar ta yi a ranar Talata, 1 ga Afrilu, 2025, ta haddasa ce-ce-ku-ce bayan da ta zargi wasu manyan jami’an gwamnati da shirin hallaka ta.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Gwamnan Kogi, Usman Ododo, sun mayar da martani, suna zargin ta da karya doka da kuma tada rikici a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kokarin kashe Natasha Akpoti-Uduaghan?
Duk da haramta taro da aka yi a Kogi ta Tsakiya, Sanata Akpoti-Uduaghan ta ziyarci mahaifarta, Okehi, inda dubban magoya bayanta suka tarbe ta cikin murna.
Sanatar ta bayyana cewa:
“Duk wani abu da ya faru da ni ko magoya bayana, alhakin na kan Akpabio, Ododo, da tsohon gwamna Yahaya Bello.”
A yayin taron, Sanatar ta kara da cewa an kitsa wani shirin kashe ta a wani taro wasu jiga-jigan siyasa suka yi, tare da kokarin ganin an janye ta daga majalisar dattawa.
Ta ce an tattara sa hannun mutane 250,000 a kwanaki biyu don kaddamar da shirin yi mata kiranye daga majalisa, wanda ta ce hukumar zabe ta INEC ce ke taimakawa wajen aiwatar da shi.
Gwamnatin Kogi ta yi wa Natasha martani
Gwamnatin Kogi ta musanta duk wasu zarge-zarge da Sanatar ta yi, tana mai cewa hakan wani yunkuri ne na tada hankali da kuma neman mutane su tausaya mata.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo, ya ce:
“Sanata Natasha ta saba amfani da karya da rudani a matsayin makamin siyasa. Tana kokarin tayar da rigima ne a Kogi ta Tsakiya, kuma ba za mu lamunci hakan ba.”
Fanwo ya ce, duk da cewa Sanatar ta goge rubutun da ta yi a Facebook, suna da kwafin abin da ta fada, wanda ke nuna cewa tana kokarin haddasa hargitsi a jihar.
A karkashin haka ya ce gwamnatin jihar ba za ta bari a yi amfani da siyasa wajen haddasa rikici ba.

Asali: Facebook
Martanin Akpabio ga Sanata Natasha
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karyata zargin cewa yana da hannu a wajen kitsa kashe Sanata Natasha.
Hadimin Sanata Akpabio, Eseme Eyiboh ya bayyana cewa ba su da lokacin yin musayar yawu da Natasha, duk da cewa abin da take fada ya nuna ba ta mutunta doka.
Shehu Sani zai nemi Sanata a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya na da aniyar tsayawa takarar majalisar dattawa a zaben 2027.
Legit ta rahoto cewa Shehu Sani ya ce zai nemi Sanata a zabe mai zuwa kwanki kadan bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng