Aronposu: Yadda 'Dan APC Ya Yaki Gawuna, Ya Taimaki Abba da NNPP a Zaben Kano

Aronposu: Yadda 'Dan APC Ya Yaki Gawuna, Ya Taimaki Abba da NNPP a Zaben Kano

  • Tsohon shugaban karamar hukuma a Kano, Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, ya bayyana cewa ya yi wa NNPP aiki a zaben gwamna
  • Aronposu ya tabbatar da cewa ya yi wa APC zagon kasa a zaben 2023, wanda hakan ya taimaka wajen karfafa nasarar Abba Kabir Yusuf
  • A karin bayaninsa kan dalilin daukar matakin, ya ce gwamnatin baya ta mayar da kananan hukumomi saniyar tatsa, aka bar su da rikon kaho

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon shugaban karamar hukuma a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, ya bayyana cewa ya yi wa Abba Gida Gida aiki a yayin neman zabe.

Ya tabbatar da cewa tabbas ya yi wa APC zagon kasa a zaben 2023, wanda hakan ya taimaka wajen karfafa nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu na zama gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Shugaban hadakar PDP ya yi Allah wadai da jita-jitar da ake yada wa kan Atiku

Aronposu
Aronposu ya tabbatar da yi wa APC zagon kasa Hoto: Sunusi Bature D-Tofa/Auwalu Lawal Shaaibu
Asali: Facebook

A wata hira da Hon Musa Caley ya wallafa a shafinsa na Facebook, Aronposu ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne domin kare martabar siyasarsa da kuma cimma burinsa a fagen siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Aronposu na zabar Abba kan APC

Sabon mataimakin darektan Shugaban hukumar KAROTA, Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta mayar da kananan hukumomi saniyar tatsa.

Ya ce a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, shugabannin kananan hukumomi sun zama 'yan rikon kaho, ma'ana ba su da cikakken iko.

A cewarsa, gwamnatin jiha ce ke amfani da su wajen cimma muradunta, maimakon barinsu su yi ayyukan da suka dace da su.

Aranposu ya ce:

"Shugabannin kananan hukumomi na lokacinmu, rakuma ne da akala. Na rikon kaho ne. Rikon kaho, wato ka rike kaho, ake tatsar saniya."

Kalaman na Aranposu ya haska zargin da ake cewa shugabannin kananan hukumomi ba su da cikakken ikon gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi martani ga Amurka kan zargin kashe kiristoci karkashin Tinubu

Aronposu ya yabi gwamnan Kano, Abba

Tsohon shugaban karamar hukumar Nasarawa, Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, ya bayyana cewa bai taba ganin gwamna mai jajircewa wajen tallafa wa talakawa kamar Abba Kabir Yusuf ba.

Gwamna
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Ya bayyana farin cikinsa da yadda APC, wacce Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi takara a cikinta, ta sha kasa a hannun al’ummar Kano a zaben da ya gabata.

A cewarsa, ya yi duk abin da zai iya a yayin neman zaben don tabbatar da cewa APC ba ta samu nasara ba.

Aronposu ya kara da cewa:

"A cikin gwamnonin da na sani, daga 1999 zuwa yanzu, babu gwamnan da ke kokarin kwatanta adalci da yin abu don al'umma face shi (Abba Kabir Yusuf)."

Aronposu ya samu mukami a gwamnatin Abba

A baya, mun wallafa cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da jerin sababbin naɗe-naɗe, daga ciki har da Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, wanda ya samu mukami a KAROTA.

Wadannan sauye-sauyen sun haɗa da shigo da ƙwararru da matasa masu ƙwazo, domin ƙarfafa aniyar gwamnatinsa ta samar da ingantaccen shugabanci da samun ci gaba a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng