"Hantar Tinubu Ta Kaɗa": An Faɗi Wanda Ya Dace Atiku, Obi da El Rufai Su Marawa Baya a 2027
- Shugaban NNPP na jihar Ondo ya buƙaci Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da sauran ƴan adawa su marawa Rabiu Kwankwaso baya a 2027
- Peter Olagookun ya bayyana cewa wannan haɗaka ta ƴan adawa za ta iya kawo ƙarshen mulkin APC idan aka tsayar da Rabiu Kwankwaso takara
- Ya yabawa tsohon mataimakin shugaban ƙasar bisa yadda yake ƙoƙarin haɗa kan ƴan adawa, ya na mai cewa tarihi ba zai manta da shi a Najeriya ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Yayin da manyan jagororin adawa ke shirin haɗaka, an fara ba da shawarwarin wanda ya dace a tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Ondo, Peter Olagookun, ya ce hadakar jam’iyyun adawa na iya samun nasara a 2027 idan manyan ‘yan siyasa sun hade kansu don fitar da dan takara guda.

Kara karanta wannan
Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

Asali: Facebook
Olagookun ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi jiya Alhamis, 27 ga watan Maris, 2025 a Akure, babban birnin jihar Ondo, kamar yadda The Cable ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nemi Atiku ya haƙura da takara a 2027
Peter Olagookun ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye daga takara kuma ya mara wa Rabiu Musa Kwankwaso baya domin kayar da APC a 2027.
A zaben 2023, Atiku (PDP), Kwankwaso (NNPP), da Peter Obi (LP) sun gwabza da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ya samu nasara.
A cewar Olagookun, idan ‘yan adawa ba su hade wuri guda baba, hadakar za ta rushe kafin babban zaɓen 2027.
Wa ya kamata Atiku, Obi su marawa baya?
Ya bukaci manyan ‘yan siyasa irin su tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Peter Obi, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai da su goyi bayan Kwankwaso domin yana da ƙarfin karawa da Tinubu.

Kara karanta wannan
Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC
"Dole ne Atiku ya janye daga takara a 2027 domin ceto Najeriya. Ya kamata ya goyi bayan dan uwansa Kwankwaso, sannan su zabi mataimaki daga kudu."
"Idan aka yi hakan, jam’iyya mai mulki ba za ta iya kai labari ba idan ta kara da hadakar ƴan adawa. Amma idan ba a hada kai ba, wannan hadaka ba za ta yi tasiri ba."
- In ji Peter Olagookun.

Asali: Facebook
Kwankwaso ya fi cancanta da takara a 2027
Olagookun ya bayyana Kwankwaso a matsayin mutum mai kima da gogewa wanda zai iya jagorantar adawa zuwa nasara a 2027.
Ya kuma jinjinawa Atiku Abubakar bisa kokarinsa na hada ‘yan adawa don tunkarar zaben 2027, rahoton Leadership.
Shugaban NNPP na jihar Ondo ya ƙara da cewa idan Atiku ya janye daga takara, tarihin siyasa ba zai manta da shi ba saboda sadaukarwarsa don ceto Najeriya.
Atiku ya yi magana kan takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba shi da tabbacin ko zai sake neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na PDP ya ƙara da cewa ana buƙatar jam'iyya mai ƙarfi domin raba APC da Bola Tinubu daga mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng