Shugabannin SDP Sun Ziyarci Mai Martaba Sarki, Ya Tsage Masu Gaskiya kan Yaudarar Jama'a
- Sarkin Ilorin, Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya karɓi bakuncin tawagar jam'iyyar SDP a fadarsa da ke jihar Kwara
- Mai martaba sarkin ya yi kira ga ɗaukacin ƴan siyasa su zama masu gaskiya da rikon amana maimakon su riƙa yaudarar ƴan Najeriya
- Shugaban tawagar SDP kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023, Prince Adebayo ya ce sun ziyarci Kwara ne domin buɗa baki da musulmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ilorin, Kwara - Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci ‘yan siyasar Najeriya da su kasance masu gaskiya da rikon amana, su daina yi wa jama’a ƙarya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar shugabannin jam’iyyar SDP ƙarƙashin jagorancin dan takararta na 2023, Prince Adewole Adebayo.

Asali: Twitter
Tawagar jam'iyyar SDP ta kai wa basaraken ziyara domin neman albarka a fadarsa da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan
Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Ilorin ya bukaci ƴan siyasa su farka
Ibrahim Sulu-Gambari ya jaddada cewa wajibi ne ga duk wani ɗan siyasa ya san mutanen da yake son mulka kuma ya fahimci halin da suke ciki.
Basaraken mai daraja ya ce:
"Ba daidai ba ne ɗan siyasa ya zauna a kusurwar wata jiha ko gari, sannan ya yi tsammanin mutane da ke sassa daban-daban na ƙasa za su zaɓe shi."
"Sannan ya kamata ‘yan siyasa su daina ƙarya ga jama’a. Idan ka kasance mai gaskiya da rikon amana, har yanzu za ka iya samun goyon bayan mutane."
Basaraken ya yabawa shugabannin SDP saboda yadda suke zaga sassan Najeriya domin fahimtar matsalolin jama’a, maimakon su jira har lokacin zaɓe ya yi.
Abin da ya sa shugabannin SDP su ka ziyarci Kwara
Tun da farko, jagoran tawagar SDP kuma ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Prince Adewole Adebayo, ya yi wa Sarkin Ilorin bayanin abin da ya kai su jihar Kwara.
Adebayo ya ce cewa sun zo Jihar Kwara ne domin su shirya buɗa baki da musulmi masu azumi kuma su halarci tarukan Ramadan tare da al’ummar Musulmi.

Asali: Twitter
Ya ce Najeriya ta na da dukiya mai yawa, amma rashin gaskiya daga shugabanni ne ke hana ci gaban ƙasar.
"A jam'iyyar SDP, burinmu shi ne mu yi wa Allah SWT hidima kuma mu yi wa al’umma," in ji shi.
A karshen ziyarar, Sarkin Ilorin ya sa wa tawagar albarka tare da addu’ar samun nasara, inda tsohon Ministan Wasanni, Cif Simon Lalong, ya kasance a cikin jerin mutanen da suka raka tawagar SDP.
Ƴan takarar gwamna sun koma SDP
A wani labarin, kun ji cewa ƴan takarar gwamna a inuwar PRP a zaɓukan da suke shuɗe sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar SDP.
Manyan kusoshin siyasar sun bi sahun tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ne da nufin ceto Najeriya daga bara-gurbin shugabanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng