El Rufai Ya Ƙara Jan Zuga, 'Ƴan Takarar Gwamna a 2023 Sun Sauya Sheka zuwa SDP

El Rufai Ya Ƙara Jan Zuga, 'Ƴan Takarar Gwamna a 2023 Sun Sauya Sheka zuwa SDP

  • Ƴan takarar gwamna a jihohi daban-daban karƙashin inuwar PRP a zaɓen 2023 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP
  • Shugaban tawagar masu sauya shekar kuma tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna, Hayatuddeen Makarfi ya ce sun koma SDP ne domin ceto Najeriya
  • Shugaban SDP na ƙasa ya yi maraba da su, ya ba su tabbacin cewa za a tafi da su ba tare da nuna banbanci ko wariya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsofaffin ƴan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar PRP a zabukan da suka gabata sun bi sahun tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai zuwa SDP.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan ficewar Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP, jam’iyyar ta samu karuwar mambobi a sassa daban-daban na Najeriya.

Malam Nasir El-Rufai.
Yan takarar gwamnonin PRP sun koma SDP, sun caccaki APC da PDP Hoto: @Elrufai
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ‘yan takarar gwamna na PRP, Mallam Hayatuddeen Lawal Makarfi, ya ce sun koma SDP ne domin ceto Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Siyasa kenan: Bayan kare El Rufai a baya, shugabar matan APC ta dawo caccakarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu na yaba wa jagoran siyasa mafi tasiri a wannan lokaci, wanda kwarewarsa da kishinsa ga Najeriya suka jawo masa matsin lamba daga masu mulki saboda tsayuwarsa a kan gaskiya."

Makarfi, wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar Kaduna a zaben da ya gabata, ya ce mutane na komawa SDP ne saboda sun yarda da shugabancinta.

Dalilin ƴan takarar na shiga SDP

A jawabinsa, Makarfi ya ce:

"A yau, mun dawo kan turba ta gaskiya, muna matukar godiya ga PRP da ta ba mu dama a siyasa, amma yau mu ƴan kungiyar ƴan takarar gwamna mun yanke shawarar shiga SDP."
"Wannan ba sauya sheka ce kaɗai ba, wani shiri ne na hadin kai domin ceton Najeriya daga mummunan shugabanci. Ba ‘yan gudun hijira ba ne mu, mun zo ne a matsayin abokan tafiya domin farfado da kasa."

Makarfi ya koka kan halin da Najeriya ke ciki, yana mai cewa, "Jini na zuba a Najeriya, talauci na karuwa, cibiyoyin gwamnati suna rushewa, yayin da APC da PDP suka maida mulki kamar kasuwanci."

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure a sakatariyar APC, matasa su kusa lakaɗawa ciyaman duka

Ya kara da cewa a zaben 2027, bai kamata ya zama tsakanin APC da PDP ba, sai dai "tsakanin Najeriya da gazawa", domin a cewarsa SDP ce kawai fatan talaka.

SDP ta yi maraba da sababbin mambobi

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Malam Shehu Musa Gabam, ya tabbatar wa sababbin mambobi cewa za a basu duk damar da ta dace bisa adalci, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa SDP ta na da aniyar sake farfado da Najeriya, tare da yin kira ga gwamnati da ta dauki matakan da suka dace domin ci gaban kasa.

"Mu na da niyyar alheri, ba sharri muke nufi ba. Ba mun zo lalata abin da aka gina ba ne, ba haka ba ne manufarmu. Amma abin da muke so shi ne mu ba gwamnati shawara domin ta yi abin da ya dace."

- In ji Gabam.

Malami ya jagoranci sauya sheka zuwa SDP

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a Katsina, Imam Nura Gwanda, ya jagoranci daruruwan masu sauya sheka daga APC da PDP zuwa jam’iyyar SDP.

Malamin ya shawarci al'umma da sauran malamai kan shiga siyasa duba da yadda ake kallonta a matsayin na lalatattun mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng