Siyasa kenan: Bayan Kare El Rufai a Baya, Shugabar Matan APC Ta Dawo Caccakarsa

Siyasa kenan: Bayan Kare El Rufai a Baya, Shugabar Matan APC Ta Dawo Caccakarsa

  • Shugabar matan jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta bi sahun masu sukar Nasir Ahmad El-Rufai saboda komawarsa SDP
  • Maryam Suleiman ta bayyana cewa komawa SDP da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi, babban kuskure ne a siyasance
  • 'Yar siyasar ta kuma caccaki manufofinsa waɗanda suka jefa mutane cikin wahala a lokacin da ya ke mulki a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shugabar mata ta jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Maryam Suleiman ta caccaki Malam Nasir El-Rufai.

Shugabar matan ta APC ta caccaki tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne saboda ficewarsa daga jam'iyyar.

Maryam Suleiman ta caccaki El-Rufai
Maryam Suleiman ta fadi kuskuren El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai, Hajiya Maryam Suleiman
Asali: Facebook

Maryam Suleiman ta soki tsohon gwamnan ne yayin da take ganawa da manema labarai a ranar Laraba, 26 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Gwamnan APC ya hango damuwa a zaben 2027

A ranar 10 ga watan Maris, Nasie El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga APC tare da komawa jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan ya buƙaci magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da su mara masa baya ta hanyar shiga jam’iyyar SDP.

Yayin da take magana da manema labarai, Maryam Suleiman ta bayyana cewa sauya sheƙar da El-Rufai ya yi babban kuskuren ne a siyasance.

Meyasa shugabar matan APC ta soki El-Rufai?

Ta soki gwamnatinsa kan wasu manufofi da suka haddasa matsaloli, musamman rushe kasuwanni da kuma korar malamai a makarantun firamare.

"Jama’a sun yi ƙorafi sosai kan waɗannan manufofi, kuma mutanen da lamarin ya shafa an tauye haƙƙokinsu."
"Wasu daga cikin waɗanda aka rushe musu kasuwanni ko kuma aka kore sun rasa rayukansu. Wasu kuma sun rasa hanyoyin samun abincinsu."

- Maryam Suleiman

Maryam Suleiman ta kuma bayyana cewa SDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, domin kuwa sabuwar jam’iyya ce da ba ta da tushe mai karfi.

Kara karanta wannan

Jerin na kusa da Buhari da jiga-jigai da ake zargin za su bar APC zuwa SDP

Ta nanata cewa tana nan daram a APC, kuma ba ta da wata niyyar barin jam’iyyar.

Maryam nemi afuwar Gwamna Uba Sani

Shugabar matan ta APC ta kuma nemi afuwar gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, kan wasu maganganun da ta yi a baya, ta na mai bayyana su a matsayin maganganun yarinta.

Maryam Suleiman shugabar matan APC a Kaduna
Shugabar matan APC a Kaduna, Maryam Suleiman Hoto: Hajiya Maryam Suleiman
Asali: Facebook

Sai dai ta amince cewa a lokacin da ta soki gwamnan, ba ta da cikakken bayani kan abubuwan da ke faruwa ne.

"Na gaya masa cewa na yi magana ne cikin rashin fahimta, kuma ban san ainihin batun ba."
"An san ni da jajircewa a jam’iyyar. Na fahimci kuskurena, kuma na yi alƙarin gyara kura-kuraina."

- Maryam Suleiman

El-Rufai ya aika saƙo ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi magana kan dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

El-Rufai ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya janye dakatarwar da ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng