Siyasar Rivers: Shugaban Riko Ya Sauke Dukkan Mutanen da Fubara Ya Nada
- Rahotanni sun nuna shugaban riko na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da duk masu rike da mukaman siyasa
- Sanarwa da aka fitar ta nuna cewa wannan mataki na daga cikin ikon da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi a matsayinsa na kantomin jihar
- Ya sauke duk masu mukamai da suka hada da sakataren gwamnati, kwamishinoni, mashawarta na musamman da shugabannin hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Shugaban riko na jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas, ya dauki matakin dakatar da duk masu rike da mukaman siyasa a jihar daga ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025.
An ruwaito cewa wannan mataki yana daga cikin hurumin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi bayan da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa gwamnan ya jaddada cewa zai yi iya kokarinsa wajen daidaita lamura a jihar musamman a bangaren zaman lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rantsar da Ibas a matsayin shugaban riko ne a ranar 19 ga Maris, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da 'yan majalisar jihar.
Hakan na zuwa ne bayan samun rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar da 'yan majalisarsa wanda ya kawo tsaiko wajen gabatar da kasafin kudin 2025.
An sauke masu mukaman siyasa a Rivers
Ibok-Ete Ibas ya bayyana cewa daga ranar 26 ga Maris, duk masu mukaman siyasa a jihar su mika ragamar ofis ga manyan sakatarorin ma'aikatunsu.
Idan babu sakatarorin kuma, to wanda ya fi kowa girma a matsayin darakta zai karbi jagoranci na wucin gadi.
Matakin na cikin abin da shugaban rikon ya yi da ya dauki hankali a kasa da mako biyu bayan ranstar da shi a jihar.
Mukaman da dakatarwar Kantoman ta shafa
Sanarwar ta bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da duk kwamishinoni.
Vanguard ta wallafa cewa sauran sun hada da shugabannin hukumomi da kwamishinoni da mashawarta na musamman da masu bada shawara na musamman.
Dalilin dakatar da masu mukami a Rivers
Tun bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, an dora nauyin tabbatar da doka da oda a kan Ibok-Ete Ibas.
Ibas ya bayyana cewa:
"Idan matsalar jihar Rivers ita ce tabarbarewar doka da oda, to aikin da ya fi cancanta a yanzu shi ne tabbatar da zaman lafiya."
A bisa haka ake ganin cewa Ibas ya dauki matakin ne domin samun damar gudanar da aikin kawo zaman lafiya da daidaita lamura a jihar Rivers.
Tun bayan dakatar da gwamna Simi Fubara ake caccakar Bola Tinubu da kiransa ya dawo da gwamnan jihar da sauran wadanda aka dakatar.

Asali: Twitter
Shugaban ma'aikatan Rivers ya yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ma'aikatan gwamnatin Rivers ya ajiye aiki mako daya bayan dakatar da gwamna Simi Fubara.
Shugaban riko na jihar, Ibok-Ete Ibas ne ya fitar da sanarwar tare da mika godiya a gare shi duk da cewa sun yi aiki ne na kankanin lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng