Rigima Ta Kaure a Sakatariyar APC, Matasa Sun kusa Lakaɗawa Ciyaman Duka

Rigima Ta Kaure a Sakatariyar APC, Matasa Sun kusa Lakaɗawa Ciyaman Duka

  • Rigima ta kaure tsakanin magoya bayan APC da shugabanni a Neja kan zaɓen ƴan takararar da za su fafata a zaɓen kananan hukumomi
  • Ƴan jam'iyyar APC sun fara zargin ana neman tursasa su wajen tsayar da ƴan takara bisa tsarin da Gwamna Umaru Bago ya kawo
  • Zanga-zanga ta zama rigima a sakatariyar APC a ƙaramar hukumar Agwara, haka nan matasa sun gargaɗi Gwamna ya sauka daga tsarinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger - Magoya bayan jam’iyyar APC sun yi zanga-zanga tare da lalata ofishin jam’iyyar saboda zargin cusa masu ‘yan takarar da ba su ƙauna a zaben kananan hukumomi.

Gwamnatin Neja karkashin jagoranci Mohammed Umar Bago ta shirya zaben ciyamomi da kansiloli a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025.

Gwamna Bago.
Rigima ta kaure a sakatariyar APC, magoya baya sun tafka ɓarna Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Gwamna Bago ya bayyana cewa APC za ta yi amfani da tsarin yarjejeniya da nasalaha wajen zaɓen ‘yan takararta, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku ya tuna baya, ya fadi dalilin kin zabar Wike a matsayin mataimakinsa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamna yake son a fitar da ƴan takara

A wani buɗa baki da ya shirya da shugabannin jam’iyyar APC, gwamnan ya ce an yanke wannan hukunci ne domin bin umarnin jadawalin zaɓe.

A tsarin, kowace karamar hukuma daga cikin guda 25 da ke jihar Neja za ta miƙa sunayen mutum uku ƴan takarar ciyaman, sai gwamna ya zabi wanda ya kwanta masa.

Zanga-zanga ta rikide zuwa rikici a APC

Sai dai wannan mataki ya fuskanci suka daga ƴan APC da ke zargin cewa akwai lauje cikin naɗi, wasu na ganin ana karɓar na goro wajen sa sunan ƴan takara.

A ranar Talata, a ƙaramar hukumar Agwara, zanga-zangar lumana ta sauya salo, fusatattun matasa suka farmaki sakatariyar APC.

A wani bidiyo da ke yawo, an ga masu zanga-zanga suna kiran, “Ba za mu yarda ba!” kafin su jefar da tutar APC da ta Najeriya tare da barnata ofishin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

Wani mazaunin garin, Mallam Abdulmalik Yunusa, ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar, Iliyasu Zakari, wanda ke neman tazarce, ya sha da kyar daga harin magoya bayan.

Galibin ƴaƴan APC da wasu jiga-jigai ba su amince shugaban ƙaramar hukumar Agwara ya yi tazarce ba, hakan ya tayar da yamutsi.

Jam'iyyar APC.
Rikicin APC ya kara kamari a jihar Neja kan shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Getty Images

Matasa sun yi barazanar ficewa daga APC

Haka zalika, a ranar Litinin, ƙungiyar matasa ta gudanar da taron manema labarai a Minna kuma ta bukaci Gwamna Bago ya janye tsarinsa na fitar da ƴan takara ta masalaha.

Matasan sun yi barazanar cewa idan har Gwamna Bago ya ƙi janye wannan tsarin, za su fara tururuwar barin jam'iyyar APC, rahoton Daily Post.

APC na kara rasa mambobinta a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa manyan kusoshi da jiga-jigan ƴan siyaaa daga APC da sauran jam'iyyu sun rungumi SDP tun bayan sauya shekar Malam Nasir El-Rufai.

Shugaban SDP na ƙasa, Shehu Gabam ya ce akalla manyan mutane 300, ciki har da tsofaffin ministoci da sanatoci sun sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng