Atiku Ya Tuna Baya, Ya Fadi Dalilin Kin Zabar Wike a Matsayin Mataimakinsa a 2023
- Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana abubuwan da suka faru waɗanda suka sanya bai yi takara tare da Nyesom Wike ba a zaɓen 2023
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce ya ɗamka ragamar komai a hannun PDP domin ta kawo masa wanda za su yi takara tare
- Atiku ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi nadama ba kan rashin zaɓar Wike a matsayin abokin takararsa a zaɓen karshe da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan yadda ya zaɓi abokin takararsa a zaɓen 2023.
Atiku Abubakar ya kuma bayyana dalilin da ya sa bai zaɓi ministan birnin tarayya Abuja na yanzu, Nyesom Wike, a matsayin abokin takararsa ba.

Asali: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da bai watsa ba a shirin talabijin mai suna Untold Stories tare da Adesuwa Giwa-Osagie, wadda jaridar Daily Trust ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hasashen Wike ya jawowa Atiku matsala
Masu nazarin al’amuran siyasa da dama sun yi amanna cewa rashin zaɓar Wike ya taka rawa wajen rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar PDP tun daga wancan lokacin.
An yi ta raɗe-raɗin cewa ƙin zaɓar Wike ya taimaka wajen rashin nasarar Atiku a zaɓen, domin tsohon gwamnan na jihar Rivers ya jagoranci wasu gwamnoni biyar na PDP wajen yi wa jam’iyyar tawaye.
Daga baya, Wike ya yi alfahari da cewa ya yi aiki don hana Atiku samun nasara, tare da sanyawa Shugaba Bola Tinubu ya lashe jihar Rivers.
Duk da haka, Atiku ya ce bai yi nadamar rashin zaɓar Wike ba a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2023.
"A’a, ko kaɗan ban yi nadama ba."
- Atiku Abubakar
Meyasa Atiku bai zaɓi Wike ba?
Da yake bayyana dalilinsa na rashin zaɓar Wike, Atiku ya nuna cewa an zarge shi da ƙin neman shawarwari sosai lokacin da ya zaɓi Peter Obi a matsayin abokin takararsa a 2019.
A cewarsa, hakan ya sanya a lokacin zaɓen 2023 sai ya ɗamka ragamar komai a hannun jam'iyya.
"Sun ce ban yi shawara da jam’iyya sosai ba. Don haka, a 2023, sai na miƙa ragamar komai a hannun jam’iyya."
"Na ce, ‘To, ku kafa kwamiti ku ba ni sunayen mutane uku da zan zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin abokin takara."
- Atiku Abubakar

Asali: Facebook
A cewar Atiku, kwamitin ya gabatar da sunayen mutum uku, tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin na farko, Wike a matsayin na biyu, sannan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, a matsayin na uku.
Atiku ya ce sai ya ɗauki na farko daga cikinsu, ya na mai cewa dalilin da ya sa bai zaɓi Wike ba shi ne domin shi ne na biyu a jerin sunayen da aka ba shi.
Atiku ya magantu kan yin takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan tskarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai da masaniya kan ko zai sake jarraba sa'arsa a 2027.
Atiku wanda bai tabbatar da cewa zai yi takara ba a 2027, ya nuna cewa a yanzu ana buƙatar jam'iyya mai ƙarfi wacce za ta kara da APC.
Asali: Legit.ng