Atiku Abubakar Ya Kawo Karshen Maganar Takararsa a 2027, Ya Fadi Shirinsa

Atiku Abubakar Ya Kawo Karshen Maganar Takararsa a 2027, Ya Fadi Shirinsa

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya taɓo batutuwan da suka shafi siyasar ƙasar nan da zaɓen 2027
  • Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai da cikakkiyar masaniyar ko zai sake neman shugabancin ƙasar nan a karo na bakwai
  • Tsohon ɗan takarar na PDP ya bayyana cewa ana buƙatar jam'iyya mai ƙarfi domin ƙoƙarin raba APC da Bola Tinubu daga mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan yiwuwar ya yi takara a zaɓen 2027.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai da masaniya kan ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 ba.

Atiku ya tabo batun takara a 2027
Atiku ya ce bai sani ba ko zai yi takara a 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da bai watsa ba a shirin talabijin mai suna Untold Stories tare da Adesuwa Giwa-Osagie, wadda jaridar Daily Trust ta samu.

Kara karanta wannan

Atiku ya tuna baya, ya fadi dalilin kin zabar Wike a matsayin mataimakinsa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya sanar da kafa haɗaka

A cikin ƴan kwanakin nan, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP, ya sanar da kafa wata haɗakar shugabannin adawa don ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Sai dai ana ta raɗe-raɗin waye zai jagoranci wannan haɗaka kuma ya zama ɗan takararta na shugaban ƙasa.

A cikin tafiyar dai akwai tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da sauran manyan ƴan siyasa.

Shin Atiku zai yi takara a 2027?

Lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a 2027, Atiku ya ce:

"Ban sani ba, saboda na farko dole ne a samu jam'iyya mai ƙarfi fiye da kowane lokaci a tarihin siyasar ƙasar nan, musamman tun bayan dawowar dimokuradiyya.”
Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa sau shida a baya, bai cire yiwuwar sake tsayawa takara a 2027 ba.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, Atiku ya fadi abin da Najeriya ta fi bukata

“Ban taɓa ganin Najeriya cikin buƙatar samun shugabanci mai nagarta kamar wannan lokacin ba."
“Muna da irin wannan haɗaka a shekarar 2014. Mu kusan huɗu ne, ko uku? Kowane ɗaya daga cikinmu ya tsaya takarar shugabancin ƙasa, ɗaya daga cikinmu ya yi nasara, muka mara masa baya, kuma ya yi nasara."

- Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya goyi bayan furucin da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi inda ya ce dimokuradiyyar Najeriya tana taɓarɓarewa, kuma lamarin ya yi muni.

“Babu kokwanto a kan hakan."

- Atiku Abubakar

Abin da Atiku yake magana a kai

Atiku ya bayyana cewa dalilin da ya sa bai yanke shawara kan tsayawa takara ba shi ne yanayin siyasar ƙasar da kuma buƙatar samun jam’iyya mai ƙarfi.

Ya ce tun bayan dawo da dimokuraɗiyya a 1999, Najeriya ba ta taɓa fuskantar irin wannan ƙalubalen siyasa ba, wanda ke buƙatar ingantaccen tsari na adawa.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

Ya kuma jaddada cewa haɗakar 'yan adawa da aka kafa za ta zama ginshikin tunkarar APC a 2027.

Atiku ya ce dole ne a kalli darasin shekarar 2014, lokacin da jam’iyyun adawa suka haɗu suka kawar da PDP daga mulki.

A kan batun tsayawa takara, Atiku ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar. Ya kara da cewa matsalolin tattalin arziki da ƙalubalen tsaro na ƙara tabbatar da buƙatar shugabanci mai nagarta.

Bugu da ƙari, Atiku ya yi kira ga matasa da su shiga siyasa, yana mai cewa canjin da ake so ba zai samu ba sai da shigar duka jama’a cikin tafiyar dimokuraɗiyya.

Atiku dai na fama da 'yan jam'iyyarsa tun bayan kammala zaben 2023 da aka yi na shugaban kasa, inda Tinubu ya lashe.

Atiku ya faɗi hanyar fitar da ɗan takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi magana kan shirin ƴan adawa dangane da babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Shirin fatattakar Tinubu ya samu cikas bayan matsayar sakataren PDP kan haɗakar Atiku

Atiku Abubakar ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa suna da tsari kan yadda za su fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya bayyana cewa ƴan adawan da ke cikin tafiyar haɗaka, za su zauna su fitar da wanda zai samu nasara kan APC.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar kara bayani a kalaman Atiku Abubakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng