Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai Za Su Zaɓi Wanda Zai Gwabza da Tinubu a 2027

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai Za Su Zaɓi Wanda Zai Gwabza da Tinubu a 2027

  • Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu matsalar da za a samu game da batun wanda haɗakar ƴan adawa za ta tsaida takarar shugaban kasa
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce za su zaɓi mutum ɗaya, sai saura su mara nasa baya kamar yadda suka yi a lokacin taron dangin 2014
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da Atiku, Peter Obi da Nasir El-Rufai ke jagorantar tattaunawar haɗakar jam'iyyun adawa gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi karin haske kan shirye-shiryen haɗakar ƴan adawa a babban zaɓen 2027 da ake tunkara.

Atiku, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023 da ya gabata, ya ce za su zauna su fitar da wanda zai samu nasara kan APC.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, Atiku ya fadi abin da Najeriya ta fi bukata

Atiku Abubakar.
Atiku ya bayyana cewa za su fitar da ɗan takarar da zai iya kayar da Tinubu a 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Getty Images

Wazirin Adamawa ya yi wannan bayanin ne a wata hira da aka yi da shi wacce aka wallafa a shafin X yau Talata, 25 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku, Obi, El-Rufai na shirin haɗaka

Idan baku manta ba jagororin adawa a Najeriya sun fara shirye-shiryen ƙulla kawancen siyasa domin kayar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Daga cikin waɗanda ake hasashen za su dunƙule wuri guda ko ma su kafa sabuwar jam'iyya har da tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi.

Sauran manyan shugabannin adawa da ka iya shiga wannan maja sun haɗa da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon ministan wasanni, Simon Dalung.

Tuni dai El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP, matakin da ake raɗaɗin yana daya daga cikin shirin da ƴan adawa ke yi na tunkarar zaɓen 2027.

A taron manema labaran da gamayyar ƴan adawan suka shirya a baya-bayan nan, Atiku ya bayyana shirinsu na kawo karshen mulkin APC.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce za su yi haɗaka da manyan ƴan adawa kuma babban burinsu shi ne daƙile shirin tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Tinubu, Obi da Atiku.
Atiku ya bayyana cewa ba za a yi rigima ba yayin tsaida dan takarar shugaban ƙaza a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

2027: Yadda ƴan adawa za su fitar da ɗan takara

A hirar da ya yi da Adesuwa Osagie Giwa, mai gabatar da shirin Untold Series yau Talata, Atiku ya ce za su fitar da ɗan takarar shugaban kasa kamar yadda suka yi a 2014.

Atiku dai na ɗaya daga cikin waɗanda suka haɗu suka kafa jam'iyyar APC bayan rusa jam'iyyun adawa da suka ƙunshi ACN, CPC, n-PDP da ANPP.

Wazirin Adamawa ya ce za su zauna da dukkan ƴan adawar da suka kulla haɗaka, su fitar da ɗan takarar shugaban kasa ɗaya wanda zai iya samun nasara a zaɓen 2027.

Atiku ya soki shugabannin Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa Atiku ya bayyana ɓacin ransa kan amincewar da Majalisun Tarayya suka yi yi da ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai yi mamaki ba sabida shugabannin Majalisar Kasar nan marasa gaskiya ne, za su iya aikata komai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng