Rikicin Ribas: Atiku Abubakar Ya Fusata, Ya Tona Cin Hancin da Ake Tafkawa a Majalisa

Rikicin Ribas: Atiku Abubakar Ya Fusata, Ya Tona Cin Hancin da Ake Tafkawa a Majalisa

  • Atiku Abubakar ya caccaki shugabannin Majalisar Tarayya kan amincewar da suka yi da matakin ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ba abin mamaki ba ne domin shugabannin Majalisar Tarayya marasa gaskiya ne
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Sanatoci da Majalisar Wakilai sun amince da bukatar Shugaban Kasa na sa dokar ta ɓaci a jihar Ribas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi shugabannin Majalisar Dokokin Tarayyya da cin hanci da rashawa.

Atiku ya bayyana shugabannin Majalisun ƙasa, Sanata Godswill Akpabio da Rt. Hon Tajudeen Abba a matsayin ƴan rashawa.

Atiku da shugabannin Majalisa.
Atiku ya zargi shugabannin Majalisun Tarayya da cin hanci da rashawa Hoto: @NGRSenate, @Atiku
Asali: Facebook

A wata hira da Adesuwa Osagie Giwa, mai gabatar da shirin Untold Series da aka wallafa a shafin X, Atiku ya soki yadda suka amince da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaƙaba a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Jerin gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu a dakatar da Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Tinubu ya sa dokar ta baci a Ribas

Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar Talata, 18 ga Maris, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar, yana mai cewa hakan ya biyo bayan ƙaruwar rikicin siyasa da matsalolin tsaro.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan 'yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Haka kuma, shugaban ƙasa ya naɗa tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral, Ibok-Ete Ibas, a matsayin shugaban rikon ƙwarya.

Bola Tinubu ya ɗora masa alhakin tafiyar da harkokin jihar ba tare da kafa sababbin dokoki ba.

Majalisar Tarayya ta amince da matakin

Bayan haka ya miƙa wannan mataki da ya ɗauka ga Majalisar Tarayya kuma dukansu biyu suka amince da bukatar mai girma shugaban kasa.

Tinubu ya yabawa shugabannin Majalisar bisa kokarinsu na tabbatar da daidaito a jihar Rivers ta hanyar amincewa da kafa dokar ta ɓaci.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

Sai dai wannan mataki ya janyo suka daga jama’a, musamman yadda aka amince da dokar ta-ɓacin ne ta hanyar ƙuri’ar murya kawai.

Atiku.
Atiku ya fusata da ƴan Majalisa suka amince da dojar ta ɓaci a Ribas Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Atiku ya zargi shugabannin Majalisa da rashawa

A cikin wata hira da Adesuwa Osagie Giwa, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki wannan mataki na Majalisar Tarayya da goyon bayan da ta bai wa Tinubu kan dokar ta-ɓacin Ribas.

Atiku ya ce:

"Ba abin mamaki ba ne, domin na san shugabannin majalisar ƴan rashawa ne, za su iya aikata komai.
"Kuma ba ɓoyayyan abu ba ne, kowa ya san Shugaban Majalisar Dattawa da irin wannan hali tun yana gwamna."

Atiku ya tabbatar da shirin ƙawancen adawa

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa sun fara shirye-shiryen haɗa kai da ƴan adawa kafin 2027.

Atiku ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai na hadin guiwa da ƴan adawa suka kira a Abuja kan abubuwan da ke faruwa a jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262