Natasha: INEC Ta Gano Kuskure a Kokarin Yi Wa Sanata Kiranye, Ta Fadi Matakin Gaba

Natasha: INEC Ta Gano Kuskure a Kokarin Yi Wa Sanata Kiranye, Ta Fadi Matakin Gaba

  • Hukumar INEC ta ki amincewa da masu neman tunbuke Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da kujerar da ta ke rike da ita a majalisar dattawa
  • Wata sanarwa da INEC ta fitar ta nuna hukumar da fake da cewa mutanen ba su bayar da adireshinsu, lambobin waya ko adireshin imel ba
  • INEC ta bayyana cewa tsarin tunbuke dan majalisa yana bisa kundin tsarin mulki, dokar zaɓe ta 2022 da ka'idojin hukumar na 2024 da ke shafinta
  • Akwai bangarori shida na takardu da suka ƙunshi sa hannun fiye da rabin masu zaɓe 474,554 a rumfunan zaɓe 902 a kananan hukumomi biyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hukumar zabe INEC ta yi martani bayan korafin masu neman yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.

Hukumar INEC ta ce masu neman tunbuke Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba su bayar da adireshinsu da lambobin waya ko imel a wasikar da suka aike wa hukumar ba.

Kara karanta wannan

Abin da Hukumar INEC ta yi kan shirin yi wa Natasha kiranye daga Majalisa

INEC ta fadi matakin gaba bayan karɓar korafin kiranye daga majalisa
INEC ta yi watsi da shirin kiranye ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan saboda kura-kurai. Hoto: Natasha H. Akpoti.
Asali: Twitter

Natasha: INEC ta gano kuskure a shirin kiranye

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin Talata, 25 ga Maris a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da kwamishinan INEC, Sam Olumekun, ya sanya wa hannu, ta ce sun yi zama kan lamarin.

Sanarwar ta ce:

“Hukumar ta gudanar da taron mako-mako yau Talata 25 ga Maris 2025, daga cikin batutuwan da aka tattauna akwai ƙorafin neman tunbuke sanatar Kogi ta Tsakiya.
“Hanyar tunbuke ɗan majalisa ta na cikin kundin tsarin mulki na 1999, dokar zaɓe ta 2022 da kuma ka'idojin hukumar na 2024 da ke shafinta.
“Hukumar za ta bi doka wajen tantance duk ƙorafe-ƙorafen da ake aikawa.”
“Takardar ƙorafin da ke fitowa daga yankin Kogi ta Tsakiya na tare da bangarori shida na takardu da aka ce sa hannun fiye da rabin masu zaɓe 474,554 ne daga rumfunan zaɓe 902 a yankunan rajista 57 da ke cikin kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.”

Kara karanta wannan

Zargin lalata: INEC ta karbi bukatar yi wa Sanata Natasha kiranye daga majalisa

An samu matsala kan shirin yi wa Sanata Natasha kiranye
Hukumar INEC ta yi watsi da shirin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye. Hoto: The Nigeria Senate.
Asali: Facebook

Natasha: Musabbabin yin fatali da korafin kiranye

Hukumar ta ce wakilan masu korafi ba su cika ka'idoji kan tsarin yadda ake kiranye ga dan majalisa ba.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Abin da hukumar ta lura da shi nan take shi ne, wakilan masu ƙorafi ba su bayar da adireshin tuntuɓa, lambobin waya ko adireshin imel a cikin wasikar da suka aiko ba kamar yadda doka ta tanada.”
“Adireshin da aka bayar shi ne ‘Okene a jihar Kogi,’ wanda ba cikakken wuri ba ne da za a iya tuntuɓarsu, an bayar da lambar waya ta ‘babban mai ƙorafi’ kawai, maimakon lambobin dukan wakilan masu ƙorafi.”
“Hukumar tana son jaddada cewa tunbuke ɗan majalisa hakkin masu zaɓe ne idan sun rasa amana a kansa.”

Hukumar ta sha alwashin bin dukan ka'idojin yin krianye da zarar an cika sharudan domin sanin matakin gaba da kuma tantancewa.

“Da zarar an cika sharuddan ƙorafi kamar yadda ka'idojinmu suka tanada, hukumar za ta fara tantance sa hannun a rumfunan zaɓe ta hanyar tsari na buɗe-ido da zaɓaɓɓun masu ƙorafi kawai za su shiga.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Zanga zanga ta barke kan takaddamar Natasha, an samu bayanai

“Masu ƙorafi da ɗan majalisar da ake so a tunbuke za su iya tura wakilansu domin su shaida tantancewar, sannan masu sanya ido da manema labarai za a ba su damar halarta.”

- Cewar sanarwar

Lauyan Natasha ya zargi gwamnatin Kogi

Kun ji cewa lauyan da ke kare Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya magantu kan yunƙurin da ake yi na raba ta da kujerarta a majalisa.

Barista Victor Giwa ya zargi gwamnatin jihar Kogi da ɗaukar nauyin masu neman yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng