Sanata Kalu Ya Watsa wa Matasan Arewa Ƙasa a Ido, Ya Yi Maganar Karawa da Tinubu a 2027

Sanata Kalu Ya Watsa wa Matasan Arewa Ƙasa a Ido, Ya Yi Maganar Karawa da Tinubu a 2027

  • Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya yi fatali da kiran matasan Arewa na ya fito takarar shugaban ƙasa a babban zabe na 2027
  • Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce ya yi imani da tsare-tsaren da Bola Tinubu ya zo da su, don haka ya na goyon bayan ya yi tazarce
  • 'Dan siyasar ya gargaɗi ƴan adawa su maida hankali a harkokin da ke gabansu, su daina tsoma shi a cikin abubuwan da suka shafe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC), Orji Uzor Kalu, ya watsawa matasan Arewa ƙasa a ido.

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi fatali da kiran da ƙungiyar shugabannin matasan Arewa (NYLF) ta yi masa na ya fito takarar shugabancin ƙasa a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Sanata Orji Kalu.
Orji Kalu ya yi watsi da kiran matasa na tsayawa takara a 2027 Hoto: Orji Kalu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Kalu ya yi watsi da tayin matasan ne a wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar ranar Lahadi, 23 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kalu, tsohon gwamnan Abia, ya bayyana cewa ba zai shiga takara ba domin ya riga ya goyi bayan tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bukatar da matasan Arewa suka mikawa Kalu

NYLF, wata kungiya da ke ƙunshe da ƙungiyoyin matasa guda 40 daga Arewa, ta bukaci Kalu da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa watau na 2027.

Ƙungiyar ta kuma roki Kalu ya ɗauki gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ko gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiri, a matsayin mataimakinsa.

NYLF ta bayyana hakan ne bayan wata ziyarar da ta kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, jihar Ogun.

Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, George Maduka, ya fitar, Kalu ya ce ya fi maida hankali kan tallafa wa Tinubu wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin da yake yi.

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

Sanata Kalu ya gargaɗi ƴan adawa

Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya bukaci ‘yan adawa da su maida hankali kan harkokinsu, maimakon ƙoƙarin jawo shi cikin tafiyarsu.

A rahoton Vanguard, sanarwar ta ce:

"Sanata Kalu ya na da ‘yancin yanke shawara kan takarar da zai tsaya, kuma takarar shugaban ƙasa a 2027 ba ta cikin shirinsa."
"Ya riga ya bayyana goyon bayan sa ga shirin tazarcen shugaba Tinubu a wa’adi na biyu kuma ya na da niyyar yin aiki don ganin an cimma hakan."
Kalu da Tinubu.
Sanata Kalu ya jaddada goyon bayansa ga Shugaba Tinubu Hoto: Orji Kalu, @OfficialABAT
Asali: Facebook

Kalu ya amince da tsare-tsaren Tinubu

Sanarwar ta ƙara da cewa Kalu ya yi imani da manufofin tattalin arzikin Tinubu, kuma yana ganin dole ne a bari ya yi shekaru takwas domin tabbatar da dorewar gyare-gyaren.

Kalu ya kuma bayyana cewa dangantakarsa da Shugaba Tinubu ta samo asali tun kafin su zama gwamnonin jihohinsu a shekarar 1999.

"Sanata Kalu mutum ne mai tsayawa kan ra’ayinsa, kuma ya riga ya yanke hukunci na marawa Tinubu baya. Zai ci gaba da goyon bayansa da kuma ƙarfafa shi kan gyare-gyaren tattalin arzikin da yake aiwatarwa," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata

Sanata Kalu ya goyi bayan ƙirƙiro jiha 1

A wani rahoton kuma, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya bayyana cikakken goyonsa kan kudirin ƙirƙiro ƙarin jiha ɗaya a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kalu, ya ce kirkiro jihar Anioma zai taimaka wajen magance tunanin da ƴan ƙabilar Igbo watau inyamurai ke yi cewa ana nuna masu wariya a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng