Akwai Matsala: SDP Na Kokarin Kawo Cikas ga Burin El Rufai na Yin Hadaka da 'Yan Adawa
- Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi watsi da batun yin haɗaka da sauran jam'iyyun adawa
- Adewole Adebayo ya bayyana cewa SDP ba za ta yi haɗaka da APC ko wata jam'iyya daban domin tunkarar zaɓen shekarar 2027
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa suna yi wa duk masu son shiga SDP maraba amma ban da masu halayen banza
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya yi magana kan shirin haɗaka da wasu jam'iyyun.
Adewole Adebayo ya yi watsi da duk wani shiri na haɗaka da jam’iyya mai mulki, wato APC ko wata jam’iyya a gabanin zaɓen 2027.

Asali: Twitter
Tashar Channels tv ta ce ya bayyana hakan ne a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyar na jihar a ranar Asabar, 22 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan
Shekarau ya fadi abin da zai faru bayan haduwar El-Rufai, Atiku kan kifar da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ziyarar, yana tare da tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, da kuma shugabannin jam’iyyar na Ogun, Oyo, da Legas, da wasu manyan ƙusoshinta.
SDP ba za ta yi haɗaka ba
Adebayo ya musanta jita-jitar da ke cewa jam’iyyarsu SDP reshe ne ko ɓangare na APC, inda ya jaddada cewa jam’iyyar ta tsaya tsayin daka kan jin dadin al’ummar Najeriya.
"Idan APC tana da cuta, to su je asibiti a yanke ta. Mu jam’iyya ce mai ƙarfi. Mun fi kowace jam’iyyar da ake da ita daɗewa. Manufarmu a bayyane take, ba mu cikin gwamnatinsu."
"Ni ne na jagoranci jam’iyyar a zaɓen da ya gabata. Har yanzu ina nan daram. Ba na riƙe da wani muƙami a ƙarƙashin Tinubu. Duk shugabannin jiha da na ƙasa suna nan daram. Don haka, muna da ƴancin kanmu."
"Dalilin da ya sa wasu ke raina mu shi ne saboda ba mu cin zarafin mutane don magance matsaloli. Jam’iyyarmu jam’iyyar masu basira ce. Tun daga shekarar 1989 da muka fito, ba mu sauya ba."
"Shin akwai wata yarjejeniya tsakanin SDP da wata jam’iyya domin yin aiki tare? Duk wanda yake son shiga SDP yana da damar haka, amma sai ya fahimci aƙidarmu. Mu jam’iyya ce da ke goyon bayan adalci da ci gaba."
- Adewole Adebayo
A ƙarshe, ya ce jam’iyyar SDP a shirye take ta karɓi sababbin mambobi masu gaskiya, amma ba mutanen da suke da alamar tambaya kan halayensu ba.
Adewole ya yabi El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya nuna murnarsa kan matakin Nasir El-Rufai na komawa jam'iyyar.
Adebayo ya bayyana Nasir El-Rufai a matsayin babbar kadara ga jam'iyyar SDP, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai tarihin shugabanci mai kyau.
Asali: Legit.ng