Gudaji Kazaure: Babban Jigo a APC Ya Gana da Atiku, Ya Fadi Shirin Kifar da Tinubu
- Alhaji Atiku Abubakar ya karɓi bakuncin Hon. Gudaji Kazaure, inda suka tattauna kan halin da Najeriya ke ciki da matakan da za a ɗauka a 2027
- Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɗin kan 'yan siyasa don ceto Najeriya, tare da samar da jagoranci da zai inganta rayuwar al’umma
- Gudaji Kazaure ya bayyana cewa sun shirya bin tsarin Atiku da shugabannin Arewa don samar da ci gaba da ceto Najeriya daga matsalolin ta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yammacin ranar Asabar, 22 ga watan Maris, 2025, Alhaji Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Hon. Gudaji Kazaure, tsohon dan majalisar wakilai daga Jigawa.
An rahoto cewa, tattaunawarsu ta ta'allaka ne kan halin da Najeriya ke ciki, tsare-tsaren yadda za a ceto Najeriya daga hannun gwamnatin APC a 2027.

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura

Asali: Twitter
Atiku ya karbi bakuncin Gudaji Kazaure
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya shaida cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A daren jiya (Asabar), na yi farin cikin karɓar bakuncin Hon. Gudaji Kazaure a gidana. Mun tattauna muhimman al’amuran ƙasa da jajircewarmu wajen inganta Najeriya."
Tsohon mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Abdul Rasheeth, ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Tattaunawarsu ta mayar da hankali kan al’amuran ƙasa, ba da fifiko kan muhimman abubuwa, da tattaunawa kan hanyoyin mayar da Najeriya zuwa ƙasa mai tarin albarka.
"Irin waɗannan tattaunawa masu ma’ana suna ƙarfafa jajircewarsu wajen gina ƙasa da kuma samar da jagoranci da zai kawo ci gaba."
Dalilin ganawar Gudaji Kazaure da Atiku
Jim kadan bayan ganawarsa da Atiku, tsohon dan majalisar wakilan, Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana dalilin ganawarsu da matsayar da suka cimmawa.
A cikin wani bidiyo da muka gani daga shafin Imran U. Wakili na X, an ji kuma an ga Gudaji Kazaure yana cewa:
"Yau na hadu da mahaifinmu, Alhaji Atiku Abubakar. Na gana da shi saboda, matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu.
"A siyasance, sai da muka tattauna da wasu shugabannin Arewa kafin muka kawo masa ziyara. Mun yanke shawarar hada kan 'yan siyasarmu domin kawo karshen matsalolinmu."
Hon. Gudaji Kazaure ya ce da yawa daga 'yan siyasar Arewa, sun watsar da al'ummarsu, sun kuma sauka daga kan turbar dawo da Najeriya zuwa kasa ta-gari.
"Da yawa daga cikin matsalolin da muka gano kuma muka fito da su fili, a lokacin gwamnatin da ta shude, ba su samu tagomashi ko kulawar shugabannin yanzu ba.
"Babu wanda zai ce ba mu bankado cin hanci da rashawa ba, amma wannan gwamnatin ba ta yi komai a kan abubuwan da muka kawo ba.
"Wannan ta sa muka yanke shawarar hado kan dukkanin 'yan siyasarmu na Arewa da ma na Kudu da ke son ci gaba, mu hada hada kai, mu tunkari yadda za mu ceto kasar mu."
"Mun shirya hada kai da Atiku" - Kazaure

Asali: Twitter
Gudaji Kazaure ya ce ya ji dadin yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya karbe shi da hannu biyu-biyu.
"Na ji dadin yadda ya karbe ni cikin mutuntawa kamar dansa, kuma ina godiya ga abubuwan da ya ce. Domin tunaninsa ya ta'allaka ne kan ci gaban Najeriya.
"Kuma duk wanda ya sanya Najeriya a gabansa, to shi ne ya kamata mu marawa baya. Don haka, mun shirya bin tsarin Atiku da na shugabanninmu na Arewa don ceto kasarmu.
"Duk abin da za mu yi, to mu sanya al'ummar mu a gaba. Kuma a shirye muke mu ba da duk wata gudunmawa don kawo ci gaba mai dorewa a Najeriya."
'Tafiyar za ta haifar da da mai ido' -Dabuwa
Kwamared Nasir Dabuwa, mazaunin Jihar Jigawa, ya yi tsokaci kan haduwar Hon. Gudaji Kazaure da Alhaji Atiku Abubakar.
Matashin dan siyasar, ya ce yanzu ƴan Najeriya sun gama karaya da gwamnatin APC, domin ta gaza sauke ko da ɗaya bisa uku na alkawuran da ta dauka.
Kwamared Dabuwa ya ce:
"Muna da kyakkyawan yakini kan nagartar Gudaji Kazaure. Kowa ya ga abin da ya yi a lokacin da yake majalisa, kuma kowa ya san fadin gaskiyarsa ya jawo suka hana shi tikitin takara.
"A bangaren adawa, Atiku ne ja gaba, sai kuma su El-Rufai da suka shigo fagen adawar yanzu. Su din ma ka ga sun zo sun yi hadaka don tunkarar 2027.
"Abin da nake so na ce shi ne, nagartar Gudaji Kazaure, da tasirin Atiku, wani abu ne da zai haifar da ɗa mai ido, kuma zamansu a inuwa ɗaya, zai sa talaka ya samu nutsuwa da su."

Kara karanta wannan
Atiku, El-Rufai, Obi da jiga jigan APC sun hadu domin shirin kifar da Tinubu a 2027
Nasir Dabuwa ya ce ma damar za a yi sahihin zabe a 2027, to ba makawa jam'iyyar APC za ta sha kayi a hannun ƴan adawa.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Al Mustapha ya ziyarci Atiku bayan komawa SDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon dogarin shugaban ƙasa a mulkin soja, Hamza Al-Mustapha, ya kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da Atiku ya tabbatar da cewa ana shirin haɗa kawancen jam’iyyu domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng