"Tinubu Ya Tsorata?": Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai

"Tinubu Ya Tsorata?": Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai

  • Fadar shugaban ƙasa ta ce Bola Ahmed Tinubu bai damu da shirin haɗakar manyan jagororin adawa a zaben 2027 ba
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Atiku, Obi da sauran masu shirin haɗa kai ba za su iya ja da Tinubu ba
  • Ya ce shugaba Tinubu ya maida hankali kan ayyukan da ke gabansa da ƙoƙarin sauke nauyin da ƴan Najeriya suka ɗora masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa manyan ƴan adawa, Atiku, Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai da ke shirin haɗewa ba za su kai labari ba.

Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce taron manyan ƴan adawar ba komai ba ne face tulin marasa nasara.

Bayo Onanuga.
Bayo Onanuga ya ce Atiku da sauran ƴan adawa ba za su iya da Tinubu ba Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan adawa na shirin haɗewa wuri guda domin tunkarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Abin da ya faru bayan Atiku Abubakar ya kammala jawabi a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku, Obi da El-Rufai na shirin haɗewa

A wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan adawa sun shirya tsaf don kalubalantar Tinubu a 2027.

Da aka tambaye shi ko taron manema labaran da ‘yan adawa suka yi na nuni da shirinsu na dunƙulewa wuri ɗaya ne, Atiku ya ce:

"Wannan shi ne farkon haɗakar ƴan adawa gabanin zaɓen 2027,"

Daga cikin jagororin ‘yan adawa da suka halarci taron akwai tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilta.

Sai kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Sakataren Gamayyar Jam’iyyun Siyasa na Ƙasa (CUPP), Peter Ameh da sauransu.

Fadar shugaban ƙasa ta maida martani

Da yake martani kan lamarin, kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya maida hankali kan harkokin shugabanci da sauke nauyin al'umma.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Onanuga ya ce:

“Shugaba Bola Tinubu ya maida hankali kan tafiyar da mulki domin gina ƙasa kuma ya na kan hanyar cimma hakan.
"Wata biyu kafin ya cika shekaru biyu a kan mulki, shugaban ƙasa na da abubuwan da zai nuna a matsayin nasarorin da ya samu.
“Matsalolin da suka jima ba a warware ba yanzu ana fuskantar su kai tsaye. Ba zai bari ya shagaltu da abin da ake kira haɗakar ‘yan siyasa ba. Ba su da wani buri na alheri ga jama’a."
Atiku Abubakar.
Bayo Onanuga ya soki manyan yan adawa da kw shirin haɗewa don kayar da Tinubu a 2027 Hoto: @Atiku
Asali: UGC

Hadimin shugaban ƙasa ya ce waɗannan ƴan adawa da ke ƙoƙarin haɗa kai ba su da wani buri na kawo ci gaba face burin kansu, Punch ta ruwaito.

"Kwaɗayin mulki ne kawai, ba don jama'a suke yi ba, cikin fushi suke, waɗannan jagororin adawar taron masu ƙashin faɗuwa ne, burinsu kawai su kayar da Tinubu," in ji shi.

Da yiwuwar Peter Obi ya koma PDP

A wani labarin, kun ji cewa alamu sun fara nuna Peter Obi na iya barin jam'iyyar LP, ya koma tsohuwar jam'iyyarsa watau PDP kafin zaɓen 2027.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan tsohon gwamnan ya ziyarci Gwamna Bala Muhammed na Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262