Yadda Akpabio Ya "Murkushe" Sanatoci da Suka Ki Amincewa Da Dokar Ta Baci

Yadda Akpabio Ya "Murkushe" Sanatoci da Suka Ki Amincewa Da Dokar Ta Baci

  • Sanata Seriake Dickson, mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a jam’iyyar PDP, ya bayyana yadda aka hana 'yan majalisa adawa da dokar ta-baci
  • Sanata Dickson ya yi zargin cewa an hana sanatoci kamar Aminu Tambuwal da Eyinnaya Abaribe da wasu daga cikin abokan fadin ra'ayinsu
  • Ya ce ya na shirin ganawa da Shugaban majalisa, Godswill Akpabio, domin bayyana rashin jin dadinsa game da hana su bayyana ra'ayinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Sanata Seriake Dickson, mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a jam’iyyar PDP, ya bayyana wasu abubuwan da suka faru a bayan fage yayin zaman majalisar dattawa kan dokar ta baci a Ribas.

Wannan mataki ya haddasa cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya, inda lauyoyi, ‘yan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama, da ‘yan siyasa suka caccaki lamarin.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

majalisa
An zargi shugaban da majalisa da hana yan adawa magana Hoto: The Nigerian Senate/Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Daily Trust ta bayyana cewa shugaba Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da kuma ‘yan majalisar dokokin Ribas na tsawon watanni shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici ya barke a majalisar dattawa

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dickson, wanda ya bar zauren majalisa kafin amincewar dokar ta-bacin, ya ce an hana Sanatoci da ke adawa da matakin yin muhawara a fili yayin zaman.

Ya bayyana cewa sanatoci kamar Aminu Tambuwal da Eyinnaya Abaribe da wasu kalilan daga cikin abokan aikinsa an toshe su daga bayyana matsayinsu a kan batun.

Dickson ya ce yana shirin ganawa da Shugaban Majalisar domin bayyana rashin jin dadinsa da hana irin wannan abu faruwa a nan gaba.

“Za a iya juyar da dokar Ribas” – Sanata

Duk da cewa majalisar dokoki ta amince da dokar ta-bacin, Dickson ya ce har yanzu bangaren shari’a na da ikon shiga tsakani.

Ya ce Majalisar dattawa wani dandali ne na ‘yan uwantaka, don haka kowanne dan majalisa na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa ba tare da neman izini daga Shugaban Majalisa ba.

Kara karanta wannan

'Me shirunsa ke nufi?' An taso Kwankwaso a gaba game da dokar ta ɓaci a Rivers

Majalisa
An zargi shugaban majalisa da dakile masu adawa da dokar ta baci Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dickson ya ce:

“A yau yayin zaman Majalisar Dattawa, an tattauna batun dokar ta-bacin da Shugaba kasa ya ayyana a Jihar Ribas. Kamar yadda na sha fadi, na bayyana matsayina a zaman sirri, inda na nuna cewa wannan mataki bai cika ka’idojin kundin tsarin mulki ba.
“Duk da cewa ba a gudanar da muhawara a bude ba, an yi tattaunawa mai zurfi. Ina gode wa Sanata Aminu Waziri Tambuwal bisa goyon bayansa ga matsayin cewa dakatar da shugabannin da aka zaba a Ribas ba bisa doka ba ne.”

Ribas: Majalisa ta amince da dokar Tinubu

A wani labarin, kun samu labarin cewa majalisar wakilai ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sanar da dokar ta-baci a jihar Ribas tare da dakatar da gwamna.

A yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, ‘yan majalisa sun amince da bukatar Shugaba Tinubu ta hanyar ƙuri’ar baki, lamarin da ke ci gaba da yamutsa hazo a siyasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.