"Ina Goyon Bayan Tinubu": Kan Gwamnoni Ya Fara Rabuwa saboda Dokar Ta Ɓaci a Ribas
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya tsame kansa daga matsayar gwamnonin Kudu maso Kudu kan dokar ta ɓaci a jihar Ribas
- Okpebholo ya bayyana cewa ya na da yaƙinin cewa matakin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka shi ne ya fi dacewa
- Tun farko gwamnonin Kudu maso Kusu sun yi watsi da ayyana dokar ta ɓaci a Ribas, sun ce hakan illa ce babba ga demokuraɗiyya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - A wani mataki mai cike da rudani, gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi magana kan matsayar wasu gwamnonin yankin Kudu Maso Kudu kan dokar ta ɓaci a Ribas.
Tun farko dai gwamnonin shiyyar Kudu maso Kudancin Najeriya sun yi fatali da dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a jihar Ribas.

Kara karanta wannan
'Suna da Sarkinsu, mu na da namu': An fadi lokacin da Aminu Ado zai yi sallar idi a Kano

Source: Twitter
Gwamna Okpebholo na jihar Edo ya nesanta kansa da wannan matsaya ta gwamnonin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Edo, Fred Itua ya fitar ranar Alhamis, 20 ga watan Maris, 2025.
Gwamnan Edo ya goyi bayan Bola Tinubu
Gwamna Okpebholo ya ce ba a tuntube shi ba ko neman shawararsa kafin takwarorinsa su bayyana matsayinsu kan batun dokar ta-baci a jihar Ribas.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya aminta da ‘yancin sauran gwamnonin yankin su fadi ra’ayinsu, amma shi bai amince da wata matsaya da ke adawa da matakin da shugaba Tinubu ya ɗauka ba.
“Shugaban ƙasa kuma kwamandan askarawan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fahimci abubuwan da ke faruwa a jihar Ribas kuma ya ɗauki matakan da suka dace domin dakile rikicin da ke ci gaba da ta’azzara.
“Gwamna Okpebholo ya na goyon bayan duk matakan da shugaba Tinubu ya ɗauka domin kawo zaman lafiya da dawwamar da kwanciyar hankali a jihar Ribas da yankin Kudu maso Kudu baki ɗaya."
- in ji Fred Itua.
Kawunan gwamnonin Kudu ya rabu
Tun bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, gwamnonin yankin Kudu maso Kudu suka nuna adawarsu da matakin, suna mai cewa cin zarafin dimokuradiyya ne.
Sai dai Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka na da tushe, kuma zai taimaka wajen dakile rikicin siyasa da ke ƙara ƙamari a jihar.
Wannan mataki da Gwamnan Edo ya ɗauka wata ɓaraka ce a ƙungiyar gwamnonin Kudu maso Kudu, wacce Ribas take mamba a ciki, The Nation ta kawo.
Ana ganin hakan ba zai nasaba da siyasa ba kasancewar Gwamna Okpebholo ɗan jam'iyyar APC ne saɓanin sauran gwamnonin jihohin Kudu maso Kudu.
Har yanzu dai ana ci gaba da samun martani daga masu ruwa da tsaki kan batun Ribas, inda wasu ke goyon bayan matakin dokar ta-baci, yayin da wasu ke nuna adawarsu.
Fubara ya musanta zarge-zargen Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya musanta laififfukan da Bola Tinubu ya ɗora masa a jawabin da ya yi.
Fubara ya jaddada cewa ya yi duk mai yiwuwa wajen kare albarkatun mai da ke jihar, kum saura ƙiris a kammala gina sabuwar Majalisar Dokoki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
