Akpabio: Kotu Ta Girgiza Natasha, Alkali Ya Sauya Hukunci kan Dakatar da Ita a Majalisa
- Wata Kotun Tarayya ta cire dokar hana Majalisar Dattawa daukar matakin ladabtarwa a kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Sanata Natasha ta shigar da kara tana kalubalantar dakatarwar da aka yi mata, amma kotu ta janye hukuncin hana Majalisa ci gaba da shari’ar
- Kotun ta bayyana cewa janye wannan doka ba za ta shafi karar Sanata Natasha ba, ta daga sauraron karar zuwa 25 ga watan Maris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kotun Tarayya da ke Abuja ta janye umarnin da ta bayar a baya na hana Majalisar Dattawa dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
A ranar Laraba ne mai shari’a Obiora Egwuatu ya janye wannan hukunci, inda hakan ya ba da damar Majalisa ta ci gaba ladabtar da Sanatar ta Kogi.

Kara karanta wannan
"Majalisa ta koma kamar kungiyar asiri," Natasha ta fadi abin da Sanatoci ke tsoro

Asali: Twitter
Rahoton Arise News ya nuna cewa Sanatar ta shigar da karar ne inda ta maka Majalisar Dattawa, shugabanta da kuma shugaban kwamitin ladabtarwa a gaban kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta dakatar da Natasha duk da umarnin kotu
A baya, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi a ranar 4 ga watan Maris, ta hana Majalisar Dattawa ladabtar da Sanatar.
Duk da hakan, a ranar 6 ga watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da ita na tsawon watanni shida, tare da rufe ofishinta da kuma umartarta da ta mayar da duk wata kadara ta majalisa.
Sanata Natasha ta nemi kotu ta hana Kwamitin Ladabtarwan Majalisa ci gaba da bincikenta, bayan samun sabani tsakaninta da Shugaban Majalisa, Sanata Godswill Akpabio.
Yadda zaman kotu ya kasance a Abuja
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan Majalisar Dattawa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ya gabatar da bukatar a janye umarnin kotun da aka bayar a baya.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Ana shirin cafke Sanata Natasha kan jawabin da ta yi a taron IPU? Bayanai sun fito
Ya ce umarnin da aka bayar a ranar 4 ga watan Maris yana da ruɗani, domin bai fayyace bangaren da aka hana yin wani aiki ba.
Ojukwu ya ce kotu ba ta da hurumin bayar da umarni mai ruɗani, ya bukaci a janye hukuncin saboda yana hana Majalisa aiwatar da aikinta na doka.
Sai dai lauyan Sanata Natasha, Michael Numa (SAN), ya bukaci kotu da ta yi watsi da bukatar janye hukuncin, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta nuna rashin mutunta umarnin kotu.
Hukuncin da kotun tarayya ta yanke
Bayan sauraron dukkan bangarori, daga karshe kotun ta cire dokar hana Majalisar Dattawa daukar matakin ladabtarwa a kan Sanata Natasha.
Alkalin kotun, Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya ce janye hukuncin hana Majalisa ladabtar da Natasha ba zai shafi karar da ta shigar ba.
Duk da haka, kotun ta ki janye zaman da aka yi a ranar 4 ga watan Maris, aka yanke hukuncin farko.
Premium Times ta rahoto cewa an dage sauraron karar da Natasha ta shigar zuwa ranar 25 ga watan Maris domin ci gaba da shari’a.

Asali: Facebook
Yadda rikicin Natasha da Akpabio ya fara
Natasha ta zargi shugaban majalisa, Akpabio da cin zarafinta tare da tauye mata hakkin gabatar da duk wasu bukatunta a gaban majalisar dattawa.
Hakazalika, ta ce ya neme ta da lalata duk da kasancewarta matar aure, lamarin da ya jawo cece-kuce, musamman daga masu rajin kare hakkin dan-adam.
Natasha ta fito gidan talabijin tare da bayyana kokenta da fadin abin da ya faru tsakaninta da Akpabio, inda ta bayyana nata sashen labarin.
Sai dai, a zaman majalisa, an dakatar da Natasha bisa zargin saba dokar majalisar, wanda ya tunzura ta da fadin wata maganar da ta kara tunzuru majalisar ta dattawa.
Ba a kan Natasha aka fara samun sabani da shugabancin majalisar dattawa ba kan wasu lamurra, an sha samun wasu batutuwa da suka shafi tauyewa wasu mambobi damar yin magana.

Kara karanta wannan
"Gwamnatin Najeriya na shirin kama ni": Sanata Natasha ta fadi halin da take ciki
Majalisa ta hargitse kan dakatar da Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa an samu yamutsi a zauren majalisar wakilai yayin da ake sa ran fara tattauna batun sanya dokar ta-baci a jihar Rivers.
Rahoton Legit ya nuna cewa an shiga rudani ne bayan shugaba Bola Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara bayan saka dokar ta-baci.
Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar waiwaye ga tushen rigimar Natasha da shugaban majalisa Akpabio a wannan shekarar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng