El Rufai Ya Fara Karɓe Magoya bayan Kwankwaso, Jiga Jigan NNPP Sun Koma SDP
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ƙara samun goyon baya a jihar Kaduna bayan sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP
- Ƴan takara akalla 200 da suka fafata a zaɓen kananan hukumomin Kaduna karkashin inuwar NNPP, sun bi sahun El-Rufai zuwa SDP
- Manyan ƙusoshin tare da dubannin magoya bayansu, sun yanke shawarar shiga jam'iyyar SDP ne domin kawo canji na alheri ga al'umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ƴan takarar kansiloli 200 na NNPP da suka tsaya takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna, tare da dubban magoya bayansu, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar SDP.
Taron sauya shekar ya gudana ne a hedkwatar SDP da ke Kaduna, inda aka yi gangamin jama'a domin shaida karɓar ƙusoshin NNPP da suka canza jam'iyya.

Asali: Twitter
Shugaban ƙungiyar masu sauya shekar, Injiniya Muhammad Yusuf Jibril ya ce sun bar NNPP zuwa SDP ne domin ceto al'umma daga halin da suke ciki, Tribune ta kawo labarin.

Kara karanta wannan
A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin jiga-jigan na bin sahun El-Rufai
A cewarsa, sun yanke shawarar shiga SDP ne saboda ita ce jam’iyyar da za ta iya samar da dimokuraɗiyya ta gaskiya ga al’umma tare da inganta walwalar talakawa.
Muhammad Yusuf ya ce:
“A matsayina na jagoran wannan tawaga, mun zo nan don tabbatar da ficewar mu daga NNPP zuwa SDP.
"Kowa ya sani cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya koma SDP, don haka mu matasa ba za mu yi kasa a guiwa ba, za mu bi shi domin ceton Najeriya da haɗin kanmu.”
“Yan takararmu sun kai 200 tare da kimanin magoya baya 10,000, duk mun amince mun dawo SDP.”
SDP za ta ceto Najeriya daga ƙunci
Haka nan sakataren ƙungiyar, Hon. Hashim Kurfi, ya bayyana cewa sun ga dacewar sauya sheƙa a wannan lokaci domin samun mafita mai kyau ga al’ummar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Bayan El Rufai ya yi fatan ya dawo SDP, alamu sun nuna Peter Obi na shirin canza jam'iyya
"Mun yanke shawarar shiga SDP domin a halin da ake ciki yanzu, wajibi ne mu zaɓi jam’iyyar da za ta kai mu ga nasara."
"Kowa ya san irin halin da matasa ke ciki a yau, babu ayyukan yi. Wannan shi ne lokacin da ya kamata mutane su zo su shiga wannan tafiya domin ci gaban al’ummar Kaduna da Najeriya gaba ɗaya.”
- Hon. Hashim Kurfi.

Asali: Twitter
Ɗaya daga cikin ƙusoshin da suka sauya sheƙar, Hon. Abdullahi Mohammed Isa, ya bayyana cewa wannan rana za ta kasance abin tunawa a rayuwarsu, domin sun koma SDP don inganta rayuwar al’umma.
“Yau wata rana ce mai muhimmanci da ba zan taba mantawa da ita ba, rana da muka haɗa kai da wata sabuwar jam’iyya domin faɗaɗa hangen nesan mu da tabbatar da ci gaban mutanenmu," in ji shi.
Jam'iyyar SDP ta zargi gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta zargi gwamnatin Bola Tinibu da APC da ƙoƙarin murkushe ƴan adawa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan
"Dama ƙarfa karfa aka mana a 2023," Sanata Tambuwal ya hango faɗuwar Tinubu a 2027
Kakakin jam'iyyar SDP na ƙasa, Rufus Aiyenigba ya zargi gwamnatin APC da amfani da jami'an tsaro wajen tsorata ƴan adawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng