"Karya ne," Shugaban PDP na Ƙasa, Damagum Ya Tattago Rigima da Ministan Tinubu
- Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya kalubalanci ministan Abuja, Nyesom Wike kan zaben shugabannin jam'iyya na Kudu maso Kudu
- Damagum ya bayyana cewa babu wani zaɓe da PDP ta shirya a shiyyar tun bayan karewar wa'adin tsofaffin shugabanni, shiyasa ta naɗa kwamitin riƙo
- An ruwaito cewa ƴan tsagin Wike a PDP sun shirya gangamin taro tare da zaɓen shugabannin jam'iyya na Kudu maso Kudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya yi fatali da zaɓen shugabannin jam'iyya na reshen Kudu maso Kudu da wasu tsiraru suka gudanar.
Damagum ya bayyana zaɓen a matsayin mara inganci, yana mai cewa babu wani sahihin gangamin zaɓe a hukumance da PDP ta shirya zuwa yanzu.

Source: Facebook
Tsagin Wike ya shirya taron Kudu maso Kudu

Kara karanta wannan
Bayan ficewar El Rufai, Ganduje ya fadi shirin APC na kwace jihohi 2 a hannun PDP
Daily Trust ta tattaro cewa tsagin PDP da ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ke jagoranta ne suka shirya taron tare da zaben shugabanni a Kudu maso Kudu.
Sun yi taron ne a jihar Kuros Riba kuma an ji Wike na cewa wannan ne kaɗai sahihin taron zaɓen shugabanni na PDP, duk wanda aka yi bayan haka ba shi da inganci.
Damagum ya ce taron Wike haramtacce ne
Sai dai, yayin da yake jawabi a wurin rantsar da kwamitin rikon kwarya na Kudu Maso Kudu a hedikwatar PDP da ke Wadata Plaza, a ranar Alhamis, Damagum ya yi fatali da taron tsagin Wike.
Shugaban PDP ya nanata cewa wa'adin tsofaffin shugabanni ya kare, don haka sai an naɗa kwamitin riƙon kwarya kafin shirya taron zaɓen shugabanni na gaba.
"Wannan taro ne mai matuƙar muhimman kuma ina amfani da wannan dama na shaida maku cewa ba mu yi wani zaɓe ba a Kudu maso Kudu.
"Ba ni da tantama a kan wannan domin wa'adin tsohon kwamitin gudanarwa na shiyyar ya kare, muna sa ran nan da wasu makonni ko watanni za mu shirya gangami.
"Hakan ya sa muka ga ya dace mu naɗa kwamitin rikon kwarya, wanda zai tafiyar da harkokin jam'iyya kafin a zaɓi sababbin shugabanni," in ji Damagum.
PDP ya naɗa kwamitin riƙon ƙwarya
Damagum ya bukaci sabbin shugabannin kwamitin riko da su yi aiki ba tare da nuna bambanci ko fifiko ba, domin tabbatar da sabon zaben shugabanni ya gudana cikin gaskiya da rikon amana.
Ya kara da cewa:
"Wasu daga cikinku na da ƙwarewa, kuma na san ku tun da dadewa. Babu shakka, za ku gudanar da ayyukanku bisa kwarewa da amana, domin tabbatar da nasarar PDP a yankin."
"Babu kamar PDP a Najeriya" - Damagum
Umar Damagum ya kara da cewa jam'iyyar PDP ta wuce tsara a tsakanin jam'iyyun siyasar da ake da su a Najeriya.
"PDP ta kasance jam’iyya mafi ƙarfi da gogewa. Tun bayan kafuwarta shekaru 27 da suka wuce, har yanzu tana nan daram.
"APC da sauran jam’iyyun siyasa da kuke gani ba su kai shekaru goma da kafuwa ba. PDP ce ke da cikakken tsarin siyasa wanda zai kawo canji a Najeriya."
- Umar Damagum.
Wike ya kira Gwamna Bala da maci amana
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya ya yi ikirarin cewa sun cimma matsaya da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed cewa za su yaƙi Atiku Abubakar a 2023 amma ya ci amana.
Wike ya jaddada cewa gwamnonin PDP da dama sun yi aiki a ɓoye don rusa jam’iyyar, musamman a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

